Marubuta tara ne suka lashe kyaututtukan ANA na baya

Spread the love

Daga AISHA ASAS

Kungiyar Marubutan Najeriya (ANA) ta sanar da sunayen marubuta tara da suka lashe kyaututtukan adabi na shekarar 2026, inda aka karrama ƙwararru a fannoni daban-daban na rubuce-rubuce.

Daga cikin waɗanda suka samu nasarar akwai fitacciyar marubuciyar nan, Oyinkan Braithwaite, wadda ta lashe kyautar ANA/King Dakolo Prize for Fiction da littafinta mai suna ‘Cursed Daughters’.

A vangaren waƙa kuwa, Jide Salawu ya samu kyautar ANA/KMVL Prize for Poetry da littafinsa na waƙoƙi mai suna ‘Contraband Bodies’.

Haka kuma, Chude Jideonwo ya lashe kyautar ANA/Sir Chukwuemeka Sam Nwelue Prize for Non-Fiction da littafinsa ‘How Depression Saved My Life’.

Sauran waɗanda suka samu kyaututtukan sun haɗa da Selome Medemaku da Bolaji Olatunde, waɗanda suka yi nasara tare a ɓangaren wasan kwaikwayo, yayin da Ekikerebong Aniekan Usoro ya samu kyautar nazarin adabi.

A ɓangaren littattafan yara kuma, Foluke Sijuwola Falayi ta lashe kyautar saboda littafinta ‘Beans for Supper’, yayin da Erhu Kome ya samu kyautar rubuce-rubucen matasa da littafinsa ‘The Smoke that Thunders’.

Haka nan, marubucin Najeriya da ke zaune a ƙasar Ireland, Deɗter Loko, ya lashe kyautar Chinua Achebe Prize for Literature da littafinsa ‘The Bako of Zereshe’, wanda ya zo da kyautar kuɗi Naira miliyan ɗaya.

Wani muhimmin sauyi da aka sanar yayin taron shi ne ƙarin kuɗin kyaututtukan ANA. Shugaban ƙungiyar, Usman Oladipo Akanbi, ya bayyana cewa daga shekara mai zuwa za a riƙa ba wa waɗanda suka lashe kowane rukuni Naira 500,000, maimakon Naira 100,000 da ake bayarwa a baya.

Wannan matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ƙungiyar ke ƙoƙarin inganta hanyoyin tallafa wa marubuta da kuma ƙarfafa harkar rubuce-rubuce a Najeriya.

By ukarofi

Leave a Reply