Gwamnatin Katsina ta sanar da sunayen ‘yan kwamitin da za su binciki Sarkin Daura

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina ta sanar da sunayen ‘yan kwamitin da za su binciki cin zarafin wata baturiya yar yawon buɗe ido da ake zargin Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk Umar da aikatawa

Mambobin kwamitin sun haɗa da Mai Shari’a Amiru Sanusi (mai ritaya) a matsayin Shugaban Kwamitin.

Sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai Dr Salisu Bala Zango ya fitar ya bayyana sauran da suka haɗa da Hon. Usman Abba – mai ba gwamna shawara kan harkokin masarautu da Mai Shari’a Sadiq A. Mahuta (mai ritaya), Galadiman Katsina, akwai kuma
Hon. Isah Dabai – kwamishinan harkokin addini da kuma tsohon shugaban ma’aikatan Jihar Alhaji Lawal Aliyu Daura da
Farfesa Halima Kabir sashen harsuna da al’adu, Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya.

Akwai Dr. Bala Salisu Zango kwamishinan yaɗa labarai da al’adu na Jihar Katsina.

Sai Hajiya Khadija Abdulkadir mai ma masarautar Belgium shawara kan harkokin diflomasiyyar tattalin arziki da Fadila Muhammad Dikko Babbar Lauya kuma kwamishiniyar shari’a ta Jihar Katsina, wadda za ta kasance sakatariyar kwamitin.

Ayyukan kwamitin sun haɗa da binciken zargin ƙoƙarin cin zarafi da ake yi wa Sarkin Daura da gayyatar duk mutanen da lamarin ya shafa ko waɗanda suke da alaƙa da zargin, gano ainihin dalilin ziyarar baƙuwar yawon buɗe ido zuwa fadar Sarkin.

Haka kuma ta binciki duk wasu takardu, bayanai da hujjoji masu alaƙa da lamarin da gudanar da duk wasu ayyuka da suka zama dole ko suke da alaƙa da tabbatar da adalci a kan lamarin.

Sai gano irin matsayin alhakin da Sarkin Daura yake da shi dangane da zargin da ba da shawarar matakan hukunci da suka dace.

Kwamitin kuma zai ba da shawarar matakan gyara da za su hana sake faruwar irin wannan lamari a nan gaba da miƙa rahoton bincikensa cikin makonni huɗu (4) daga ranar ƙaddamar da aikin kwamitin.

Ana sa ran kwamitin zai fara gudanar da aikinsa nan take bayan ƙaddamar wa, sannan ya miƙa rahotonsa cikin wa’adin da aka ƙayyade.

Kwamishinan ya yi kira ga al’umma da su ba kwamitin damar gudanar da aikinsa cikin ’yanci ba tare da matsin lamba ba. Haka kuma, an buƙaci jama’a da su guji duk wani aiki ko furuci da zai iya kawo cikas ga binciken ko kuma ya shafi gudanar da aikin kwamitin.

Gwamnati ta kuma tabbatar wa jama’a cewa za a tabbatar da adalci bisa sakamakon binciken da kwamitin zai gabatar.

By ukarofi

Leave a Reply