Tinubu ya jinjina wa gudunmawar Atiku a dimukraɗiyya, ilimi da kasuwanci yayin cikarsa shekaru 80

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar da taya tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Alhaji Atiku Abubakar murnar cikarsa shekaru 80 a duniya a ranar Laraba, 25 ga Nuwamba, 2026, inda ya kuma yaba wa gudunmawarsa ga ci-gaba da nasarorin da Nijeriya ta samu a sanadiyyarta.

Tinubu, a saƙonsa na zagayowar ranar haihuwa, ya tunatar da tsawon shekaru na hidimar siyasa a tsakaninsu da ƙoƙarin tafiyar da harkokin dimukraɗiyya, musamman a lokacin da ya bai wa Atiku goyon baya a takarar shugaban ƙasa na zaɓen 2007 a tsohuwar jam’iyyar Action Congress.

Saƙon, wanda je ɗauke da sanya hannun Shugaba Tinubu, ya ce goyon bayan ya nuna yadda suka yi fafutukar nasarori ga dimukraɗiyya a lokacin da aka bai wa ‘yan siyasa damar shiga da samar da mafita na hangen nesa kan muhimman al’amuran ƙasa da bayar da gudumawa kan jagoranci da shugabancin ƙasa.

Ya ƙara da cewa, tsohon Mataimakin Shugaban ƙasar ya riƙa kira ga siyasa mai tsafta, da buɗe ƙofar sulhu bayan bambance-bambance ko rashin jituwa da ‘yan adawar siyasa.

Shugaban ya kuma bayyana gudunmawar Atiku a ilimi, kasuwanci da fannin kamfanoni na masu zaman kansa a matsayin abin a yaba, yana mai cewa shigar a harkokin ci-gaban kasuwanci da zuba sun taimaka wajen samar da damarmakin tattali da ayyuka ga ‘yan Nijeriya.

Musamman shugaban ya jinjina wa Atiku bisa samar da jami’ar American University of Nigeria, Yola, wadda a cewarsa ta taimaka wajen faɗaɗa hanyoyin samun ilimi mai nagarta a matakin manyan makarantu da ƙarfafa lamuran inganta ɗan-adam.

Ya kammala saƙon nasa da: “Barka da cika shekara 80 ya Mai Girma.”

By Babaji