Daga SULEIMAN HUSSAINI D /KUDU a KANO
An bayyana mauludi a matsayin wani muhimmin abu da a ko yaushe yake ƙarawa masu yin sa ƙauna da soyayyar Manzon Allah da kuma tunawa da irin baiwar da Allah ya yi masa.
Malamin addinin musuluncin nan Malam Sa’idu Ahmad Gidan Nagunda ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da ‘yan jaridu a wajen mauludin zawiyar Raudatu Zawiyati Sheikh Ahmad Yahaya Lil-Dhikr, Wal-ta-Lim-wal-Irshad da ta saba gudanarwa a duk shekara karo na 21 a ranar Juma’a a filin zawiyar da ke garin Dawakin kudu.
Malamin yace mauludi lokaci da ake ƙara nuna soyayyar fiyayyen halitta a fili tare da tunatar da al’umma da su ringa tunawa da irin wannan gwaggwaɓar ni’ima da Allah ya yiwa mutane wanda a cewarsa, Allah bai taba wata halitta ba kamar Manzon Allah(SAW).
Ya kuma ja hankalin al’umma wajen kula da masu nunawa cewa yin mauludi bashi da amfani tare da yin kira gare su da su rinƙa lura da irin makarantu da za su rinƙa sanya ‘ya’yan su don gujewa irin waɗannan matsalolin.
Shima da yake nasa bayanin wanda ya ke shirya mauludin a duk shekara Malam Naziru Ahmad Gidan Nagunda yace suna shirya mauludin ne sabo da girman Allah da yi masa godiya da ya sake nuna musu wannan lokacin. Inda yace a duk lokacin da suka tashi shirya irin wannan mauludi suna cike da farin ciki da jin daɗi.
Ya kuma miƙa godiyar sa ga waɗanda suka samu halartar taron mauludin tare da fatan alkhairi a gare su.
