
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumomin Saudiyya sun sanar da kama wasu ‘yan Nijeriya guda biyu a yankin Riyadh bisa zargin su da ayyukan safara da dillancin tabar wiwi da wasu ƙwayoyin ƙara kuzari da kuma mallakar wasu magunguna da ba su samu sahalewar amfani ba daga hukumomin lafiya.
Jami’an Cibiyar Tsaro ta Mujahideen ne suka aiwatar da atisayen, wanda ya yi sanadiyyar kama mutanen akan zargin su da hannu a safarar haramtattun ababe masu bugarwa.
Ajil, wadda jarida ce ta ƙasar Saudiyya, ta ruwaito a ranar Laraba cewa an samu mutane biyun da wasu ƙwayoyi da aka sanya su a ajin masu sanya maye da ba a amince da amfani da su ba a hukumance. Jaridar ta ce an kama su kuma an damƙa su ga hukumomin da suka dace, inda aka fara gudanar da ayyukan shari’a akansu.
Akan haka ne Mujahideen ta yi kira ga al’umma da su riƙa ruwaito dukkan wasu waɗanda ake zargi da fasa-ƙwauri da dillancin miyagun ƙwayoyi ta lambobin da hukumomi suka samar a sassan ƙasar. A cewar Ajil, mazauna Makkah, Medina, Riyadh da Lardin Gabas za su iya ruwaito da labaran da suka shafi dillancin ƙwayoyi ta 911, yayin da ‘yan wasu shiyyoyi kuma za su aike da saƙonninsu ta 999 da 995.
Wannan kame na zuwa ne yayin da hukumomin Saudiyya ke gudanar da atisaye akan masu safara da dillancin miyagun ƙwayoyi a sassan ƙasar.
