Daga AISHA ASAS
Bikin littattafai da fasaha na Lagos (Lagos Book and Art Festival), wanda aka fi sani da LABAF, ya buɗe ƙifa a ranar Litinin, 16 ga Nuwamba, 2026, inda aka fara shirye-shiryen da za su haɗa marubuta, masu fasaha, masu wallafa littattafai da sauran masu ruwa da tsaki a harkar adabi.
Bikin na wannan shekara, wanda shi ne bugu na 28, yana gudana ne ƙarƙashin taken REPAIR: The Workover Starts Now, inda aka tsara gudanar da shirye-shirye daban-daban har zuwa ranar 22 ga Nuwamba.
ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi jan hankali a bikin shi ne bikin cika shekaru 35 da kafuwar ƙungiyar Committee for Relevant Art (CORA), wadda ta assasa bikin LABAF a shekarar 1999.
Haka kuma, bikin ya tanadi wani shiri na musamman domin girmama fitaccen mawallafin wasan kwaikwayo kuma mawaƙi, Femi Osofisan, wanda ya cika shekara 80 a wannan shekara.
A cikin shirye-shiryen, an tanadi zaman tattaunawa kan rubuce-rubucensa, waƙoƙinsa da kuma gudunmawar da ya bayar ga bunƙasa adabin Najeriya.
Bugu da ƙari, an tsara tattaunawa ta musamman kan cikar shekara 40 da marubucin Najeriya, Wole Soyinka, ya lashe kyautar Nobel ta adabi a shekarar 1986.
Wani ɓangare da zai ja hankalin masu bibiyar harkar rubuce-rubuce shi ne taron da aka ware domin nazarin yadda fasahar ƙirƙirar basirar na’ura (AI) ke sauya harkar wallafa littattafai, wanda za a gudanar a ranar 19 ga Nuwamba.
Haka kuma, bikin zai ƙunshi karatun littattafai, baje kolin zane-zane, wasan kwaikwayo, tarurrukan marubuta da shirye-shiryen ƙarfafa sha’awar karatu a tsakanin matasa da ɗalibai.
Masu shirya bikin sun bayyana cewa za a gudanar da shirye-shiryen ne a wurare daban-daban da suka haɗa da Freedom Park da J. Randle Centre, tare da ba da damar halarta ta yanar gizo.
Bikin na daga cikin manyan tarukan adabi da fasaha da ake gudanarwa a Najeriya, musamman wajen haɗa ƙwararru da sababbin masu tasowa a fannin rubuce-rubuce da sauran ayyukan fasaha.
