
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Kula da Harkokin Ingancin Abinci da Magani ta Ƙasa NAFDAC, ta rufe kasuwar Zuba a Abuja biyo bayan atisayen tabbatar da biyayya ga doka da jami’anta suka gudanar inda suka bincika shaguna sama da 160 kuma suka ƙwace kayayyaki na jimillar sama da Naira miliyan 300.
Atisayen, wanda aka gudanar bisa haɗin-gwiwar jami’an ‘yan sanda da hukumar DSS, wani ɓangare ne na kawo ƙarshen siyar da gurɓatattun kaya da marasa inganci ko amfani acikin al’umma yayin da ake tunkarar bukukuwa ƙarshen shekara.
Da yake ganawa da ‘yan jarida bayan atisayen, Shugaban Sashen Bincike reshen Arewa ta Tsakiya, Pharm. Babatunji Omoyeni, ya ce an gudanar da atisayen ne ƙarƙashin ƙoƙarin da NAFDAC take yi wajen bayar da kariya ga lafiya da amincin ‘yan Nijeriya.
A cewarsa, Darakta-Janar ta hukumar, Farfesa Mojisola Christianah Adeyeye ce ta bayar da umarnin kakkaɓe dukkan wasu gurɓatattun kayayyaki daga kasuwannin faɗin ƙasar, musamman a lokacin bukukuwan ƙarshen shekara da buƙatun kwastomomi suke ƙaruwa. Omoyeni ya ce NAFDAC za ta cigaba da aiki tuƙuru wajen tabbatar da bada kariya ga al’umma daga amfani da kayayyaki masu haɗari ga lafiya da amincinsu.
Ya kuma kirayi ‘yan Nijeriya da su kasance masu kula da aika wa hukumar dukkan wani rahoton abin zargi a yankunansu da zai taimaka mata wajen gano mutane, wuraren da ake samarwa, ajiyewa, rabawa da siyar da lalatattu da kaya maras inganci acikin al’umma.
Kazalika, ya jinjina wa rundunar ‘yan sanda da DSS bisa bayar da haɗin kai da taimakonsu wajen atisayen, yana mai bayyana muhimmancin haɗin-gwiwa a tsakanin hukumomin ƙasar wajen aiwatar da harkokinsu ta yadda hakan ke taimakawa wajen samun kyawawan sakamako.
