
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamna Mohammed Umaru Bago na Jihar Neja a Arewa ta Tsakiyar Nijeriya, ya tabbatar da cewa kimanin mutane 74 ne suka rasu a faɗace-faɗacen tsakanin ‘yan bijilanten Kambari da Fulani makiyaya a Ƙaramar Hukumar Borgu ta jihar, inda ya umarci a gudanar da bincike mai zurfi kan rikicin da kuma sanar da bayar da tallafin jimillar Naira miliyan 148 ga iyalan da al’amarin ya shafa.
Bago ya bayyana haka ne yayin ziyarar gaisuwar ta’aziyya da ya kai wa Sarkin Borgu, Alhaji Halilu Sani Ɗantoro a fadarsa da ke garin New Bussa, wato hedikwatar ƙaramar hukumar, inda ya jajenta wa basaraken da al’ummar masarautar kan abin alhinin.
Wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun ƙaddamar da wani hari bayan rikicin a ƙauyen Lumman-Ba’are a ranar Asabar da ta gabata a lokacin da aka halaka Mai garin yankin, Mallam Bawa Muhammad, matarsa da ‘ya’yansa uku. Maharan sun kuma cinna wa gidan mai garin wuta kafin su tsere, kamar yadda Manhaja ta ruwaito.
Gwamnan ya umarci a gaggauta gudanar da bincike kan rikice-rikicen domin gano waɗanda suke da hannu a ciki da ainihin musabbabin aukuwar al’amarin, sannan da yadda suke hakan ke faruwa akai-akai domin kauce musu a nan gaba. Akan haka ne Bago ya kirayi ‘yan ƙauyukan da fitinar ta shafa da su ɗauki matakan zaman lafiya a tsakaninsu, haƙuri da juna da fahimtar juna, yana mai cewa ba a samun ci-gaba a guri muddin ana samun rikice-rikice da rashin jituwa acikin al’umma.
Da yake bayyana alhininsa ga iyalan mamatan, gwamnan ya sanar da bayar da tallafin Naira miliyan 2 ga kowane ɗaya daga cikin iyalai 74 da abin ya shafa, wanda ya kai adadin kuɗin da za a ba su zuwa Naira miliyan 148. Kazalika, ya yi alƙawarin samar musu da kayan abinci da na gine-gine domin tallafa wa mazaunan da aka lalata wa gidaje a sanadiyyar rikice-rikicen.
A ƙarshe, ya yaba wa Majalisar Masarautar Borgu bisa ƙoƙarinta na samar da zaman lafiya da haɗin kai acikin al’umma, yana mai kira ga ‘yan Nijeriya da su koyi zama a waje guda ba tare da la’akari da bambance-bambancen da ke tsakaninsu ba.
