Daga JOHN D. WADA a Lafia
Jihar Nasarawa ta bi sawun al’ummar duniya wajen bikin ranar duniya ta kawar da cin zarafi kan mata da kuma ƙaddamar da kamfen na kwana 16 na yaƙi da cin zarafin jinsi na 2026.
Kamfen ɗin wanda zai gudana daga 25 ga Nuwamba zuwa 10 ga Disamba, 2026, yana da taken “Haɗe Kai” don kawo ƙarshen cin zarafi kan mata da ‘yan mata: Tabbatar da adalci, kare waɗanda suka tsira, kawo ƙarshen rashin hukunci.”
Da take magana da manema labarai a wajen ƙaddamarwar a ofishinta da ke Lafia a ranar Alhamis kwamishinar ma’aikatar harkokin mata da cigaban zamantakewa na jihar Hon. Rebecca Adamu Kpadji ta ce taken na bana kira ne ga dukkan masu ruwa da tsaki da su ƙarfafa tsarin adalci, su kare waɗanda suka tsira, kuma su tabbatar da cewa ana hukunta masu aikata laifin.
Kwamishinar ta lura cewa cin zarafin jinsi ya kasance babban abin damuwa na haƙƙin ɗan Adam da lafiyar jama’a, inda daya cikin mata uku da ‘yan mata a duniya ke fuskantar cin zarafi a rayuwarsu.
Tace baya ga illolin jiki da na zuciya, waɗanda suka tsira galibi suna fuskantar ƙyama, wariya, wahalar tattalin arziki da kuma tsoron bayar da rahoto game da abin da suka fuskanta.
A Jihar Nasarawa, ta ce lamarin yana buƙatar kulawa mai ɗorewa da kuma haɗin gwiwa. Tsakanin Janairu zuwa Satumba 2026, Jihar ta samu rukunin laifukan cin zarafin jinsi daban daban guda 888 da aka bayar da rahoto idan aka kwatanta da rukuni 852 a cikin wannan lokacin a 2025.
Ta ƙara da cewa ƙaruwar ta nuna buƙatar ƙarfafa matakan rigakafi, bayar da rahoto, tallafawa waɗanda suka tsira da kuma matakan ɗaukar nauyi a faɗin jihar.
Kpadji ta yaba wa abokan ci gaba, ƙungiyoyin aiwatarwa da masu ba da hidima ga GBV saboda ci gaba da jajircewarsu wajen tallafawa waɗanda suka tsira ta hanyar kula da lafiya, ba da shawara ta fuskar tunani, shiga tsakani na tsaro da kuma taimakon shari’a.
Tace gudummawar su ta kasance mai matuƙar muhimmanci wajen ƙarfafa tsarin mayar da martani na jihar.
A matsayin wani ɓangare na kamfen na kwana 16 na bana, ma’aikatar, tare da haɗin gwiwar abokan aikinta za ta gudanar da ziyarar wayar da kai a al’ummomi da makarantu, tattaunawa da manema labarai da kuma ayyukan wayar da kan jama’a.
Kamfen ɗin zai kuma haɗa da tafiyar haɗin kai a faɗin jihar, wadda za ta kammala da wani babban taro don tattara goyon bayan jama’a kan dukkan nau’ikan cin zarafin jinsi.
Kwamishinar ta kuma jaddada cewa kawo ƙarshen GBV ba nauyin gwamnati kaɗai ba ne, tana mai lura da cewa iyaye, makarantu, cibiyoyin gargajiya da na addini, shugabannin al’umma, matasa da manema labarai duk suna da muhimmiyar rawa da za su taka.
Saboda haka ta yi kira ga dukkan mazauna Jihar Nasarawa da su ƙi amincewa da cin zarafi, su yi magana kan cin zarafi, su tallafa wa waɗanda suka tsira kuma su tabbatar da cewa ba a kare masu aikata laifi da shiru ko tasirin zamantakewa ba.
“Yayin da muke ƙaddamar da kamfen na bana, bari mu sabunta alƙawarin mu na haɗin gwiwa na gina al’umma inda kowace mace da ‘yar mata za ta iya rayuwa cikin aminci, mutunci da kuma ‘yanci daga cin zarafi,” in ji ta.
“Tare za mu iya tabbatar da adalci, kare waɗanda suka tsira da kuma kawo ƙarshen rashin hukunci a Jihar Nasarawa.” Inji ta.
