NAHCON ta fayyace matsayin masu ajiyar kuɗin Hajjin 2027 da rabon gurabe

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Alhazai ta Nijeriya (NAHCON) ta bayyana cewa rage yawan guraben aikin Hajjin 2027 da Saudiyya ta yi ya samo asali ne daga ƙarancin wuraren da za a iya bai wa maniyyata.

Hukumar ta ce biyan cikakken kuɗin aikin Hajji ba ya tabbatar wa maniyyaci samun gurbi, domin rabon guraben yana dogara ne da adadin da Saudiyya ta ware wa Nijeriya.

NAHCON ta bayyana cewa masu ajiyar kuɗin Hajjin 2027 da suka cika sharuddan cancanta amma ba su samu gurbi ba, za su samu fifiko wajen rabon guraben Hajjin 2028, bisa la’akari da adadin guraben da za a ware wa Nijeriya da sauran ƙa’idojin aikin Hajji.

Hukumar ta ce waɗannan maniyyata na da zaɓin neman a mayar musu da kuɗinsu ta hannun bankunan da abokan hulɗar tsarin ajiyar kuɗin Hajji (HSS) ke amfani da su, ko kuma su bar kuɗin a matsayin ajiyar Hajjin 2028.

Ta kuma shawarci waɗanda suka zaɓi ci gaba da ajiyar kuɗinsu su kammala biyan kuɗin Hajjin 2028 kafin ƙarshen aikin Hajjin 2027.

NAHCON ta ƙara da cewa tana aiki kan samar da kundin bayanan aikin Hajji na ƙasa, wanda zai taimaka wajen inganta tsarin tattara bayanai da gudanar da aikin Hajji.

Hukumar ta buƙaci maniyyata da sauran masu ruwa da tsaki su riƙa samun sahihan bayanai ta kafafen sadarwarta na hukuma.

By ukarofi

Leave a Reply