Sojoji sun kuɓutar da mutum biyar da aka sace a Kaduna

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Dakarun Sojojin Nijeriya sun kuɓtar da mutum biyar da wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Jihar Kaduna, ciki har da wata mata da jaririnta, bayan maharan sun yi watsi da su yayin da suke tserewa daga farmakin sojoji. Haka kuma, sojojin sun cafke wasu mutum biyu da ake zargi da ta’addanci a wasu hare-haren yaƙi da ta’addanci daban-daban da suka gudanar a ƙaramar Hukumar Chikun ta jihar.

An gudanar da waɗannan samame ne a ranar Laraba, 25 ga Nuwamba, 2026, bayan samun kiran neman agajin gaggawa kan hare-haren ’yan ta’adda da sace-sacen mutane a al’ummomin Dan Bushiya da Kakura.

A cikin wata sanarwa da Kyaftin Tamuno Sinivie, muƙaddashin jami’in yaɗa labarai na rundunar Operation FANSAN YAMMA, ya fitar, ya bayyana cewa dakarun sun yi artabu da maharan a wani ɓangare na aikin kuɓutar da mutanen, amma hakan bai hana su ci gaba da gudanar da aikin ba, kuma babu wanda ya rasa ransa. Aikin farko ya biyo bayan harin da wasu ’yan bindiga da ake zargin ’yan ta’adda ne suka kai wa al’ummar Dan Bushiya, inda suka yi awon gaba da wasu mazauna yankin. Siniɓie ya ce sojojin sun yi artabu da maharan tare da tilasta musu tserewa, inda suka bar wata mata da jaririnta a wurin. Daga bisani, dakarun suka kuɓutar da su.

A wani samame na daban kuma, sojojin sun mayar da martani ga wani kiran neman agaji bayan wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da mazauna ƙauyen Kakura guda biyar. Sanarwar ta ce hanzarin da sojojin suka yi wajen kai ɗauki ya tilasta wa maharan tserewa, inda suka bar mutum uku daga cikin waɗanda suka sace. Sojojin sun kuɓutar da mutanen uku. Rundunar sojin ta bayyana cewa tana ci gaba da haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro domin bin sawun maharan da suka tsere, tare da kuɓutar da duk sauran mutanen da ka iya kasancewa a hannunsu.

A wani labari makamancin haka, dakarun da ke gudanar da aikin bincike da kuɓutar da mutanen da aka sace a Dan Bushiya sun gano katin shaidar ɗan ƙasa a kan hanyar da ake zargin maharan suka bi wajen tserewa. Bayan gano katin, sojojin sun cafke wanda katin yake ɗauke da sunansa, mai suna Shauibu Musa, tare da wani mutum mai suna Aliyu Ahmed. Rundunar sojin ta ce tana tsare da mutanen biyu domin gudanar da ƙarin bincike a kansu.

Rundunar Operation FANSAN YAMMA ta sake jaddada aniyarta ta yaƙi da ta’addanci da sauran ayyukan ta’addanci da aikata laifuka a yankin Arewa maso Yamma. Ta kuma yi kira ga mazauna yankunan da su riƙa sanar da hukumomin tsaro bayanan da suka dace kuma ingantattu a kan duk wani motsi ko hali da suke zargi.

Haka zalika, rundunar ta buƙaci al’ummomin yankin da su ba da goyon baya ga ayyukan sojoji da sauran hukumomin tsaro da ake gudanarwa domin dawo da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

By ukarofi

Leave a Reply