
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wasu ma’aurata da aka yi garkuwa da su tare da jaririyarsu mai kimanin wata shida daga gidansu da ke unguwar Millennium City a jihar Kaduna, sun roƙi hukumomin tsaro su ceto su daga halin da suke ciki.
Sun yi wannan magiya ne a wani faifan bidiyo da ke nuna mijin mai suna Ahmed Abubakar Zakka ɗauke da ‘yar tasu da matarsa zaune a gefensa, inda ɗaya daga cikin masu garkuwar yake nuna musu bakin bindiga. A ranar 6 ga Oktoba, 2026 ne aka yi awon-gaba da su, a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai farmaki a yankin Rukunin Gidajen Alrahus da ke Millennium City a Ƙaramar Hukumar Chikun ta jihar.
Maharan sun afka wa yankin ne da misalin ƙarfe 11:30 na dare inda suka riƙa shiga gida-gida suna binciken waɗanda za su yi garkuwa da su. An sace Zakka da matarsa da jaririyar ne bayan ‘yan bindigar sun kutsa cikin gidansu. Da yake jawabi a harshen Hausa a bidiyon mai tsawon daƙiƙa 40, Zakka ya bayyana cewa, masu garkuwar suna buƙatar a biya su kuɗin fansar sako su na Naira miliyan 300.
Haka kuma, ‘yan bindigar sun sace wata mata mai juna biyu a lokacin da mijinta Abdulƙdir Bello yake Abuja a yayin faruwar al’amarin.
Bello ya bayyana cewa matarsa ta kira shi a daren inda ta sanar da shi abin da yake faruwa gabanin maharan su riske ta, lamarin da ya sa ya gaggauta kiran ‘yan sanda, amma kasancewar bai same su ba sai ya kira sojoji, waɗanda suka hanzarta tura jami’ai zuwa yankin. Daga bisani, maharan sun sace matar sannan suka kira shi akan batun biyan kuɗin fansa.
Wannan al’amari ya faɗaɗa matakin fargaba akan hare-hare da garkuwa a yankin Millennium City da unguwannin da ke kewayensa a wajen cikin garin Kaduna, sakamakon an sha samun hare-haren garkuwa a yankin.

