Lokaci ya yi da za a tsabtace rundunar ’yan sandan Nijeriya gaba ɗaya

Spread the love

A duk ƙasashen da suka ci gaba, babu wata hukuma da ta fi muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya, kare rayuka da dukiyoyi da kuma tabbatar da bin doka kamar rundunar ‘yan sanda. Ita ce fuskar gwamnati da talaka ya fi haɗuwa da ita a rayuwarsa ta yau da kullum. Saboda haka, ingancin aikin rundunar ‘yan sanda na da tasiri kai tsaye kan yadda jama’a ke kallon gwamnati da kuma tsarin adalci.

A Nijeriya kuwa, duk da irin ƙoƙarin da gwamnati da shugabannin rundunar ke yi wajen sake fasalin aikin ‘yan sanda, har yanzu akwai wasu ɓata-garin jami’ai da ke ci gaba da lalata martabar wannan hukuma mai daraja. Waɗannan mutane kaɗan ne suke jefa tabo ga dubban jami’an da ke aiki cikin gaskiya da kishin ƙasa.

Abin takaici ne yadda wasu jama’a ke jin tsoron zuwa ofishin ‘yan sanda domin neman taimako, maimakon su ji cewa sun isa wajen samun kariya. Wannan ba saboda dokar ƙasa ba ce, sai dai saboda munanan ɗabi’un wasu jami’ai masu cin zarafin aikinsu.

Ana ci gaba da samun koke-koke kan karɓar cin hanci, tilasta biyan kuɗaɗen beli duk da cewa dokar ƙasa ta bayyana ƙarara cewa “Beli kyauta ne” (Bail is Free). A wasu wurare, mutum ba zai iya karɓar takardar beli ko ganin wanda ake tsare da shi ba sai ya biya kuɗi, sai ka ce za a saya wani abu, abin takaici!

Haka kuma, ana samun rahotannin wasu jami’ai da ke buƙatar kuɗi kafin su karɓi ƙorafi daga wanda aka zalunta. Wannan ya sa wasu talakawa su daina neman haƙƙinsu saboda rashin kuɗin da ake nema ba bisa doka ba.

Wani abin damuwa shi ne yadda a wasu lokuta ake kama mutane ba tare da cikakken bincike ba, ko kuma a tsare su tsawon lokaci ba tare da gurfanar da su a kotu ba. A wasu lokutan kuma, ana sakin wanda ake zargi da aikata babban laifi saboda tasiri ko kuɗi, yayin da marasa galihu ke ci gaba da zama a tsare.

Ba za a manta da lokutan da aka samu rahotannin mutuwar mutane yayin da suke tsare a hannun jami’an tsaro ba, ko kuma mutanen da aka yi musu duka da azabtarwa domin tilasta musu amsa laifin da ba su aikata ba. Irin waɗannan abubuwa sun sa aka taɓa gudanar da zanga-zangar #EndSARS, wadda ta nuna irin damuwar al’umma kan cin zarafin wasu jami’an tsaro.

Akwai kuma lokutan da ake ganin wanda ya fara kai ƙara shi ne ake ɗauka a matsayin mai gaskiya tun kafin a gudanar da cikakken bincike. Wannan ya saɓa wa ƙa’idar adalci, domin doka ta tanadi cewa dole ne a saurari ɓangarorin biyu kafin a yanke hukunci ko ɗaukar wani mataki.

Hakazalika, akwai lokutan da ake amfani da ofisoshin ‘yan sanda wajen sasanta rikice-rikicen bashi, matsalolin kasuwanci ko rikicin iyali ta hanyar da ba ta dace ba, maimakon a bi hanyoyin doka.

Duk waɗannan matsaloli ba wai suna cutar da jama’a kaɗai ba ne, suna kuma lalata sunan rundunar baki ɗaya. Jami’an kirki da ke aiki dare da rana domin kare ƙasa su ne ke shan suka saboda kuskuren wasu tsirarun marasa kishin aiki.

Sai dai, duk da waɗannan ƙalubale, dole ne a yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa ci gaba da nuna aniyarsa ta inganta harkokin tsaro da ƙarfafa hukumomin tsaro domin su yi aikinsu yadda ya kamata. Ina kuma yaba wa Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Nijeriya, IGP Olatunji Rilwan Disu, saboda ƙoƙarin da yake yi na aiwatar da sauye-sauye a rundunar, ƙarfafa horo, da kuma ɗaukar mataki kan jami’an da aka samu da laifukan karya doka.

Sai dai gyara ba zai kammala ba matuƙar ba a tabbatar da cewa duk jami’in da aka kama da cin hanci, karɓar kuɗin beli, azabtar da mutane, kashe wanda ba shi da makami ba bisa ƙa’ida ba, ko kuma amfani da aikinsa wajen zaluntar jama’a, ya fuskanci hukuncin doka cikin gaggawa.

Sai dai kuma, kamar yadda Hausawa ke cewa, “Ba a taru an zama ɗaya ba.” Duk da irin koke-koken da ake yi kan halayen wasu ɓata-garin jami’ai, akwai ɗimbin jami’an ‘yan sanda masu gaskiya, riƙon amana da sadaukar da kai wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma. Bai kamata kuskuren wasu tsiraru ya sa a manta da irin gudunmawar waɗannan nagartattun jami’ai ba, domin su ne ginshiƙin mutuncin rundunar.

ɗaya daga cikin irin waɗannan jami’ai shi ne Kwamishinan ‘Yan Sanda, Usman Shugaba, wanda sunansa ya yi fice a bakin jama’a saboda kyakkyawar mu’amalarsa da mutane, biyayya ga doka da kuma jajircewarsa wajen gudanar da aiki cikin adalci da mutunci. Irin wannan shugabanci ne ya kamata ya zama abin koyi ga sauran jami’ai, domin yana nuna cewa za a iya aiwatar da aikin ɗan sanda cikin ƙwarewa, tausayi da girmama haƙƙin ɗan Adam ba tare da kauce wa doka ba. Irin waɗannan jami’ai ne ya kamata gwamnati ta ƙara ƙarfafawa da yabawa, domin su ne ke dawo da amincewar jama’a ga Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya.

Ya kamata a ƙarfafa sashen kula da ladabtar da jami’an ‘yan sanda domin ya kasance mai cin gashin kansa wajen bincike. Haka kuma, dole ne sakamakon binciken irin waɗannan koke-koke ya kasance a fili domin jama’a su ga cewa babu wanda ya fi ƙarfin doka.

Hakanan akwai buƙatar ƙarin amfani da na’urorin zamani kamar kyamarorin da jami’ai ke sanyawa a jikinsu yayin aiki (body cameras), tsarin karɓar koke-koke ta intanet, da kuma wayar da kan jama’a game da haƙƙoƙinsu idan suka shiga ofishin ‘yan sanda.

Ya dace gwamnati ta ƙara inganta walwalar jami’an ‘yan sanda ta hanyar albashi mai kyau, inshora, gidaje da kayan aiki na zamani. Duk da cewa rashin walwala ba hujja ba ce ta cin hanci ko zalunci, inganta rayuwar jami’ai zai rage wasu daga cikin matsalolin da ke haifar da rashin ɗa’a.

Har ila yau, shugabannin rundunar su tabbatar da cewa ana ba jami’ai horo akai-akai kan haƙƙin ɗan Adam, dabarun gudanar da bincike na zamani, da hanyoyin mu’amala da jama’a cikin mutunci da girmamawa.

ƙasa ba za ta iya samun cikakken ci gaba ba idan jama’a suka daina amincewa da hukuma mafi kusa da su wajen tabbatar da doka. Da zarar mutane sun rasa amincewa da ‘yan sanda, hakan na iya sa wasu su fara ɗaukar doka a hannunsu, abin da zai ƙara dagula tsaro.

Saboda haka, wannan lokaci ne da ya kamata gwamnati ta ƙara ƙaimi wajen cire ɓata-garin jami’ai daga cikin rundunar tare da ba nagartattun jami’ai cikakken goyon baya. Hakan zai dawo da martabar rundunar, ya ƙarfafa amincewar jama’a, kuma ya tabbatar da cewa adalci yana aiki ga kowa ba tare da nuna bambanci ba.

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya cibiya ce ta tabbatar da doka da oda. Kare mutuncinta ba yana nufin a rufe ido ga kura-kuranta ba ne; a’a, yana nufin a gyara kura-kuran domin ta zama abin alfahari ga ‘yan Nijeriya. Idan aka ɗauki matakan da suka dace cikin gaggawa, babu shakka za a samu rundunar da jama’a za su riƙa gudu zuwa gare ta domin neman kariya, ba wai gudu daga gare ta saboda tsoro ba.

Lokaci ya yi da za a tabbatar cewa doka tana aiki ga kowa, har ma ga masu aikin tabbatar da doka. Wannan ne kaɗai zai ƙarfafa adalci, ya bunƙasa zaman lafiya, kuma ya sake gina amincewar al’umma ga Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya.

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD. 07066778190.

By ukarofi

Leave a Reply