12
Mar
Rahoton da Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta bayar kwanan nan kan alƙaluman farashin kayan masarufi (CPI) abin damuwa ne matuƙa. Rahoton ya ce jadawalin tashin farashi a Nijeriya ya ƙaru da kashi 12.82 cikin ɗari a watan Yuli da ya gabata, kuma ba a taɓa ganin irin wannan tashin ba a cikin watanni 27 tun daga watan Maris na 2018 lokacin da farashi ya yi bala’in tashi da kashi 13.34 cikin ɗari. Wannan yanayin zai ƙara tavarɓarar da fatara da yunwa da ake ciki, wanda hakan kuma bazarana ce ga Shirye-shiryen Agajin Jama’a (SIPs) waɗanda Gwamnatin Tarayya ke aiwatarwa,…
