Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban Hukumar Yaƙi da Masu Yi wa Tattalin Arziƙin ƙasa Zagon ƙasa (EFCC), Mista Ola Olukoyede, ya yi alƙawarin bai wa masu fallasa bayanai a faɗin duniya lada tsakanin kashi 2.5 zuwa 5 cikin 100 ga duk wanda ya bayar da sahihin bayani da zai taimaka wajen gano tare da kwato kuɗaɗe ko dukiyoyin Nijeriya da ake zargin ’yan Nijeriya masu rashawa sun wawashe suka kai ƙasashen waje.
Olukoyede ya yi wannan kiran ne ranar Laraba yayin gabatar da jawabi a taron ƙasa da ƙasa karo na 43 kan laifukan tattalin arziki da aka gudanar a Cambridge, Birtaniya.
Shugaban EFCC ya buƙaci duk wanda ke da bayanin inda aka kai ko aka ɓoye dukiyar Nijeriya a ƙasashen waje da ya fito ya sanar da hukumar, yana mai tabbatar da cewa za a ba shi ladan kuɗi idan aka samu nasarar kwato dukiyar.
In ji shi, duk wanda ya bayar da bayanin da ya kai ga kwato dukiyar zai samu lada tsakanin kashi 2.5 zuwa 5 cikin 100 na abin da aka kwato.
Olukoyede ya ƙara da cewa wasu daga cikin waɗanda za su bayar da irin waɗannan bayanai na iya zama hamshakan attajirai sakamakon ladan da za su samu.
Ya bayyana cewa cikin shekaru uku da ya jagoranci EFCC, hukumar ta samu kwace da tabbatar da ƙwace kuɗaɗe da kadarori da darajarsu ta haura dala miliyan 500 ga gwamnatin Nijeriya.
Ya danganta nasarorin da hukumar ta samu da ƙwarewa da ƙwarewar masu binciken EFCC, ƙarfafan tsarin shari’a da kuma samun sahihan bayanan sirri.
Shugaban EFCC ya kuma bayyana cewa tsarin ƙwace dukiya ba tare da sai an samu hukuncin dauri ba a Nijeriya na bai wa hukumar damar neman ƙwace kadarorin da ake zargin an samu su ne daga aikata laifi, ba tare da jiran kammala shari’ar laifin ba.
Ya ce irin wannan tsari yana kama da tsarin da ake amfani da shi a ƙasashe irin su Australia da Canada.
