Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Fadar Shugaban ƙasa ta zargi tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da bayar da bayanai masu karo da juna kan shirinsa na dawo da tallafin man fetur idan aka zaɓe shi a matsayin Shugaban ƙasa a 2027.
Aminiya
Mai bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya ce Atiku da mataimakansa sun bayar da bayanai daban-daban kan yadda shirin dawo da tallafin zai kasance cikin mako guda.
A cewar Onanuga, mai magana da yawun Atiku, Paul Ibe, ya fara cewa gwamnatin Atiku za ta dawo da tallafin man fetur na wani lokaci kafin daga bisani ta cire shi a hankali.
Sai dai wani babban mataimakin Atiku, Phrank Shaibu, ya ƙi amincewa da wannan bayani, yana mai cewa ba za a sanya lokacin da za a daina biyan tallafin ba.
Ya ce za a ci gaba da biyan tallafin har sai matatun mai na cikin gida sun ƙaru tare da samar da mai cikin farashi mai sauƙi.
Daga baya, Atiku ya jaddada cewa yana kan bakansa na dawo da tallafin domin rage wa ’yan Nijeriya wahala da matsin rayuwa.
Fadar Shugaban ƙasa ta bayyana bayanan daban-daban da aka bayar a matsayin ruɗani, tare da buƙatar Atiku ya bayyana yadda tallafin zai yi aiki.
Ta nemi ya bayyana waɗanda za su amfana da tallafin, yadda za a samar da kuɗin tallafin da kuma lokacin da za a daina biyan shi.
Onanuga ya ce ’yan Nijeriya na buƙatar ingantaccen tsarin tattalin arziƙi mai cikakken bayani, ba alƙawuran siyasa domin neman goyon bayansu a zaɓen 2027 ba.
