NNPCL ya ƙara farashin fetur zuwa N1,270 duk da rangwamen Dangote na kai kaya kyauta

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Kamfanin Nigerian National Petroleum Company Limited (NNPCL) ya ƙara farashin litar man fetur (PMS) daga N1,250 zuwa N1,270 a gidajen mai na kamfanin da ke Abuja da kewaye.

ƙarin N20 ya zo ne duk da shirin matatar Dangote na raba fetur ba tare da kuɗin jigilar kaya ba zuwa wasu wurare 10 a Nijeriya, ciki har da Abuja, inda ake sayar da litar kan N1,185.

Wani binciken kasuwa da aka gudanar a Abuja ya nuna cewa farashin fetur ya bambanta daga gidan mai zuwa wani, inda ake sayar da litar tsakanin N1,230 da N1,299.

Kamfanin MRS ma ya ƙara farashin litar fetur da N20 zuwa N1,230.

A halin yanzu, farashin NNPCL ya fi na wasu gidajen mai kamar MRS, Geregu, Ranoil, Emedab da Mobil tsakanin N15 zuwa N40 kan kowace lita.

ƙarin farashin na zuwa ne yayin da farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya ke raguwa. A lokacin da aka fitar da rahoton, ana sayar da gangar ɗanyen man Brent kan kusan dala $88.80, yayin da WTI ke kan kusan dala $81.86.

ƙarin matatun mai na cikin gida da sauye-sauyen farashin ɗanyen mai na ci gaba da yin tasiri kan kasuwar man fetur ta Nijeriya, yayin da masu ababen hawa ke sa ido kan sauye-sauyen farashin lita.

By ukarofi

Leave a Reply