Gwamnatin Kano ta ƙara mafi ƙarancin fansho daga N5,000 zuwa N20,000

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin Jihar Kano ta ƙara mafi ƙarancin kuɗin fanshon da ake biyan ma’aikatan da suka yi ritaya daga N5,000 zuwa N20,000 a wata.

Shugaban ƙungiyar ’Yan Fansho ta Nijeriya (NUP), reshen Jihar Kano, Shuaib Musa-Jibrin, ne ya bayyana hakan a wata hira da Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) a Kano.

Musa-Jibrin ya ce ƙarin kuɗin fanshon ya biyo bayan tattaunawa tsakanin gwamnatin jihar da wakilan ’yan fansho.

Ya kuma bayyana cewa gwamnatin Kano ta samu ci gaba wajen biyan basussukan alawus-alawus da sauran hakkokin ’yan fansho.

A cewarsa, daga cikin bashin da aka gada wanda ya kai kusan N48.6 biliyan, gwamnatin ta riga ta biya kusan N32 biliyan, yayin da ake ci gaba da shirin biyan sauran bashin.

Shugaban NUP ɗin ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta samu ci gaba wajen biyan fanshon wata-wata a kan lokaci, inda ’yan fansho ke karɓar hakkokinsu tsakanin ranakun 23 zuwa 25 na kowanne wata.

Haka kuma, Musa-Jibrin ya yaba da matakin gwamnatin na dakatar da wasu cire-cire daga fanshon ’yan ritaya, yana mai cewa matakin ya ƙara musu kwarin gwiwa da sauƙaƙa musu rayuwa.

By ukarofi