Babban Sakataren NLC, Emmanuel Ugboaja, ya rasu jiya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Babban Sakataren ƙungiyar ƙwadago ta Nijeriya (NLC), Kwamred Emmanuel Ugboaja, ya rasu yana da shekaru 60 bayan fama da doguwar jinya.

An bayyana rasuwar Ugboaja ne a jiya Alhamis, yayin da Majalisar Zartarwa ta ƙasa ta NLC ke gudanar da taro a Enugu.

Rahotanni sun ce, Shugaban NLC, Kwamred Joe Ajaero, ne ya sanar da mambobin majalisar labarin rasuwar bayan iyalan marigayin sun aika da wasiƙar sanarwar rasuwar.

Kwamred Ugboaja, wanda ƙwararren lauya ne kuma gogaggen ɗan ƙungiyar ƙwadago, ya zama Babban Sakataren NLC na biyar a watan Agustan 2019, inda ya gaji Peter Ozo-Eson.

Ya shafe sama da shekaru 30 yana aiki a fagen ƙwadago, tun bayan da ya shiga harkar ƙungiyoyin ma’aikata a shekarar 1993, bayan ya kwashe kusan shekaru huɗu yana aikin lauya a kamfanoni masu zaman kansu.

An haifi Ugboaja ranar 15 ga Mayun 1966. Ya karanci shari’a a Jami’ar Calabar, inda ya samu digirinsa na fannin shari’a a shekarar 1987.

Daga baya ya shiga ƙungiyar Ma’aikatan Masana’antun Sinadarai, Takalma, Roba, Fata da Kayayyakin da ba na ƙarfe ba, inda ya yi ta hawa matakan shugabanci har ya zama babban sakatarenta daga shekarar 2000 zuwa 2005.

Tarihin NLC ya bayyana Ugboaja a matsayin lauyan Najeriya na farko da ya sadaukar da kansa gaba ɗaya wajen yi wa ƙungiyar ƙwadago aiki.

Baya ga ayyukansa na ƙungiyar ma’aikata, ya taka rawa a harkokin ƙungiyoyin fararen hula, tare da shiga cikin muhimman matakan sake fasalin kundin tsarin mulkin Nijeriya a shekarun 2005 da 2014.

Kafin a naɗa shi Babban Sakataren NLC, Ugboaja ya riƙe matsayin Mataimakin Babban Sakataren NLC, sannan ya jagoranci Sashen Hulɗar Ma’aikata da Tsara ƙungiyoyi na majalisar ƙwadagon.

A lokacin da yake jagorantar babban sakatariyar NLC, Ugboaja ya kasance cikin masu taka muhimmiyar rawa a tattaunawar ƙungiyar da gwamnati kan batutuwan da suka shafi ma’aikata, ciki har da aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi da walwalar ma’aikata.

Rasuwarsa ta jefa ƙungiyar ƙwadagon Nijeriya cikin jimami, musamman ganin irin gudunmawar da ya bayar wajen wakiltar muradun ma’aikata da kuma bunƙasa harkar ƙwadago a ƙasar.

By ukarofi

Leave a Reply