Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su yi riƙo da koyarwar Annabi Muhammad (SAW), musamman wajen kyautatawa, zaman lafiya, haƙuri, adalci da haɗin kai.
Idris ya bayyana hakan ne a saƙonsa na taya Musulmi murnar zagayowar Maulidin Annabi Muhammad (SAW), inda ya ce bikin wata dama ce ta tunawa da kyawawan halaye da koyarwar Manzon Allah.
Ya ce waɗannan halaye suna da muhimmanci musamman a lokacin da Nijeriya ke fuskantar sauye-sauyen tattalin arziki da sauran ƙalubale.
Ministan ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya, ƙarƙashin jagorancin Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, na ci gaba da aiwatar da sauye-sauye da suka shafi ƙarfafa tattalin arziki, inganta tsaro, samar da ababen more rayuwa da faɗaɗa damar samun ilimi da sana’o’i.
Ya buƙaci ’yan Nijeriya da su kasance masu haƙuri, sadaukarwa da haɗin kai wajen gina ƙasa mai tsaro, kwanciyar hankali da wadata.
Haka kuma, Idris ya yi kira ga al’umma da su kula da marasa galihu tare da taimaka wa masu buƙata, yana addu’ar Allah Ya ƙara wa Nijeriya zaman lafiya, tsaro da wadata mai ɗorewa.
