Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Shugaban ƙaramar Hukumar Dala, Hon. Surajo Imam, ya yaba da ƙoƙarin fitaccen ɗan kasuwar gasashen naman rago, Alhaji Malami Mai Nama, wajen samar wa matasa ayyukan yi da kuma bunƙasa harkar kasuwanci a Jihar Kano.
Surajo Imam ya bayyana hakan ne a wajen buɗe wani sabon katafaren wajen sayar da gasashen naman rago na Alhaji Malami Mai Nama, da ke kan Titin Ibrahim Taiwo a Kano, ranar Laraba.
Ya ce kasuwanci na ci gaba da bunƙasa a Jihar Kano, yana mai cewa Alhaji Malami ya fara sana’ar ne da tallan nama a kwano, kafin daga bisani ya samu matsuguni a Sansanin Alhazai, sannan ya faɗaɗa sana’ar zuwa sassa daban-daban na jihar.
Shugaban Dala ya bayyana cewa sabon wajen shi ne na tara da Alhaji Malami ya buɗe, yana mai cewa hakan wata alama ce ta ci gaba da jajircewa da bunƙasar kasuwancinsa.
“Ta yadda yake samar wa matasa aiki a wajen sayar da namansa, yana taimaka wa gwamnati wajen rage zaman banza. Musamman yanzu, sana’ar fawa ba ta tsaya ga wanda ya gada ba, kowa na iya shiga. Har da Fulani yanzu suna yi. Wannan dama ce da arziki zai ƙara bunƙasa a Kano,” inji shi.
Surajo Imam ya kuma danganta nasarar Alhaji Malami da biyayya da kyautatawa ga iyayensa, yana mai cewa biyayya ga iyaye na daga cikin abubuwan da ke kawo nasara a rayuwar mutum.
A nasa jawabin, Alhaji Malami Mai Nama, wanda ya kafa wajen sayar da naman mai suna “Hajj Camp”, ya gode wa al’ummar Kano bisa karamci da yadda suke karɓar baƙi da kuma ɗaukar su tamkar ’yan gari ba tare da bambanci ba.
Ya kuma yaba wa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa kulawar da yake bai wa bunƙasar kasuwanci, tare da turo wakilci zuwa tarukansu.
Alhaji Malami ya yi kira ga matasa da su jajirce wajen neman na kansu, yana cewa ya shafe sama da shekaru 35 yana gudanar da sana’ar sayar da nama a Kano, tun zamanin mulkin Ibrahim Babangida.
Ya ce ya riƙa shiga kasuwannin Singer, Kantin Kwari, Sabon Gari, Ujule da Kasuwar Sansanin Alhazai, kafin Allah Ya ba shi damar kafa nasa wurin.
“Amma matasa ba sa iya tsayawa su jajirce su nemi kuɗi yanzu. Sai suna tunanin su samu kaya mai kyau ko mota nan take. Wannan ba ya samuwa sai da aiki tuƙuru da yin haƙuri, gaskiya, riƙon amana da biyayya ga iyaye,” in ji shi.
A nasa ɓangaren, ɗaya daga cikin abokan Alhaji Malami, Alhaji Abdu Yandoma, ya bayyana shi a matsayin mutumin kirki mai kyautatawa al’umma.
Yandoma ya ce Alhaji Malami na da ma’aikata sama da 100, yana mai cewa yana kula da ’yan’uwa, abokai da masu buƙata, tare da tsayawa kan gaskiya da riƙon amana.
“Hatta ma’aikatan gwamnati ba lallai ne su samu albashin da yake biya ba,” in ji Alhaji Abdu Yandoma.
Manyan ’yan kasuwa, jami’an gwamnati da jami’an tsaro daga sassa daban-daban ne suka halarci bikin buɗe sabon katafaren wajen sayar da gasashen naman Alhaji Malami Mai Nama da ke kan Titin Ibrahim Taiwo, Kano.
