Kiran da Mai Martaba Sarkin Kano, Dakta Muhammadu Sanusi II, ya yi ga Ƙungiyar Tarayyar ƙasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS) da ta sasanta da ƙasashen Nijar, Burkina Faso da Mali abin dubawar shugabannin yankin ne. Kira ne da aka yi da hikima da hangen nesa a daidai lokacin da yankin Afrika ta Yamma yake fuskantar manyan ƙalubalen tsaro, tattalin arziki da siyasa waɗanda ba a taɓa ganin irin su ba. Maimakon a bar saɓanin ra’ayi ya rikiɗe zuwa rarrabuwar kai ta dindindin, ya kamata ƙungiyar ECOWAS ta yi amfani da kowace dama wajen dawo da aminci da sake gina haɗin kan yankin, wanda shi ne babban ƙarfin ƙungiyar tun kafuwar ta. Ficewar da Nijar, Mali da Burkina Faso suka yi daga ƙungiyar a ranar 29 ga Janairu, 2025, bayan sun bayar da sanarwar shekara guda, tana ɗaya daga cikin manyan koma-bayan da ƙungiyar ta taɓa fuskanta. Wannan mataki ba zai amfani ECOWAS ba, haka kuma ba zai amfani su ma ƙasashen uku ba.
Idan an tuna, gwamnatocin sojin ƙasashen uku dai sun fice ne bayan an shafe shekaru uku ana rashin jituwa wanda ya fara tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijar a watan Yulin 2023. ECOWAS, ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ta ƙaƙaba wa Nijar takunkumin tattalin arziki mai tsauri, har ma ta yi barazanar amfani da ƙarfin soja domin dawo da mulkin farar hula. Mali da Burkina Faso, waɗanda su ma suka dawo ƙarƙashin mulkin soja bayan juyin mulki, suka bayyana cewa za su ɗauki duk wani hari kan Nijar a matsayin ayyana yaƙi a kan su. Wannan taƙaddama ta ƙara haifar da rashin aminci a tsakanin ɓangarorin, har ta kai ga ƙasashen uku suka kafa Ƙawancen ƙasashen Sahel (AES) kafin daga bisani suka fice gaba ɗaya daga ECOWAS.
Duk da yake ECOWAS ta ɗauki waɗannan matakai ne domin kare aƙidar ta ta hana sauyin gwamnati ba bisa tsarin mulki ba, abubuwan da suka biyo baya sun nuna cewa takunkumi kaɗai ba zai iya tabbatar da haɗin kan yanki ba. Kamata ya yi diflomasiyya ta riƙa barin ƙofa a buɗe domin yin sulhu. Yayin da rabuwar take ƙara tsawaita, haka ma asarar da kowane ɓangare yake fuskanta yake ƙaruwa. Ana iya cewa zargin da ƙasashen uku suka yi na cewa tsauraran matakan takunkumin tattalin arziki da abin da suka kira tsoma bakin siyasa ne suka sa suka fice, yana nuna cewa su ma suna jin raɗaɗin wannan rabuwar, kuma za su fi so a sake karɓar su cikin ƙasashen ‘yan’uwan su na ECOWAS.
Saboda haka, shawarar da Sarkin Kano ya yi ta zo a kan kari kuma tana da muhimmanci. Kalaman sa daidai ne cewa rashin kasancewar ƙasashen Sahel uku a cikin ECOWAS yana raunana haɗin kan yankin, yana kawo cikas ga haɗin gwiwar tsaro, tare da rage damar bunƙasar tattalin arziki a Afrika ta Yamma. Maganar da ya yi cewa, “haɗuwar ƙasashe 15 ta fi haɗuwar ƙasashe 12,” sun bayyana ainihin manufar ECOWAS. Ana kafa ƙungiyoyin yanki ne domin haɗin kai, ba domin a ware wasu ba.
Wataƙila hujja mafi ƙarfi da Sarkin ya gabatar ita ce ta fuskar tsaro. Nijar tana da muhimmin matsayi tsakanin Nijeriya da manyan yankunan da ke fama da rashin tsaro a Libya da Aljeriya. Tsawon shekaru, Nijeriya ta dogara ne da haɗin gwiwa da Nijar wajen musayar bayanan sirri, sintirin kan iyakoki da yaƙi da ta’addanci. Hare-haren Boko Haram, ISWAP da sauran ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi kamar Lakurawa da kuma ‘yan bindigar da ke addabar wasu jihohin Arewa sun nuna sau da dama cewa ta’addanci ba ya mutunta iyakokin ƙasa. Duk wani rauni a tsarin tsaron yanki yana bai wa masu safarar makamai, ƙungiyoyin masu aikata laifuffuka da ‘yan ta’adda damar cin gajiyar iyakokin da ba su da cikakken tsaro.
Sarkin ya kuma tunatar da ‘yan Nijeriya tarihi. A lokacin Yaƙin Basasar Nijeriya, ƙasar Nijar ta tsaya tsayin daka wajen goyon bayan Nijeriya duk da matsin lambar ƙasashen duniya. Bai kamata a manta da irin wannan goyon bayan ba. Dangantakar ƙasa da ƙasa ba ta dogara ga yarjejeniyoyi kaɗai ba, har ma da zumunci mai ɗorewa da aka gina tsawon shekaru. Kare irin wannan dangantaka na buƙatar haƙuri, mutunta juna da kuma diflomasiyya mai amfani.
Har ila yau, akwai hujja mai ƙarfi ta fuskar tattalin arziki. Kano ta daɗe da zama ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin kasuwanci na Yammacin Afrika, inda ‘yan kasuwa daga Nijar, Mali, Burkina Faso, Chadi da sauran ƙasashe suke haɗuwa. Dubban ‘yan kasuwa, masu sufuri, masana’antun kayayyaki da manoma suna dogara da kasuwancin da ke gudana cikin walwala tsakanin ƙasashen nan. Katsewar waɗannan hanyoyin kasuwanci na kaka da kakanni a dalilin saɓanin siyasa yana jefa talakawa cikin wahala ta hanyar rasa hanyoyin samun kuɗaɗen shiga, hauhawar farashi da ƙanƙancewar kasuwanni. Nijeriya za ta fi cin gajiyar dawo da wannan dangantaka a matsayin ta na ƙasa mafi girman tattalin arziki a yankin. Maƙwabtan da ke zaman lafiya da juna za su faɗaɗa kasuwancin kayayyakin Nijeriya, ƙarin damar zuba jari da kuma haɓaka samar da abinci da makamashi. A gefe guda kuma, ci gaba da ware juna yana iya sa kasuwanci ya karkata zuwa wasu tsare-tsare da za su rage muhimmancin tattalin arzikin ECOWAS.
Gargaɗin Sarkin Kano game da haɗarin watsi da haɗin kan yanki abin dubawa ne idan aka duba abin da ya faru a wani sashen na duniya. Misali shi ne ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai (Breɗit). Ficewar ta nuna cewa rabuwar siyasa tana iya haifar da dogon tasiri maras daɗi na tattalin arziki da gudanarwa fiye da yadda aka zata. Ko da yake haɗin kan yanki ba ya rasa ƙalubale, ba kasafai rusa shi yake haifar da sakamako mai kyau ba.
Yin sulhu ba yana nufin ECOWAS ta yi watsi da aƙidojin ta na kare dimokiraɗiyya ba ne. Tilas ne ƙungiyar ta ci gaba da kare tsarin mulki da bin doka. To amma tarihi ya nuna cewa tattaunawa ta fi doguwar gaba tasiri wajen warware rikice-rikicen siyasa. Mu’amala da gwamnatocin soja ba yana nufin amincewa da juyin mulki ba ne, illa hanya ce ta cimma matsaya da dawo da mulkin dimokiraɗiyya a ƙarshe. A yau, Afrika ta Yamma tana fuskantar matsalolin ta’addanci, sauyin yanayi, ƙarancin abinci, hijira ba bisa ƙa’ida ba da kuma manyan laifukan da suka shafi ƙasashe da dama. Babu wata ƙasa da za ta iya shawo kan waɗannan ƙalubale ita kaɗai. Haɗin gwiwar yanki yana da matuƙar muhimmanci.
Sarkin Kano ya kawo mafita mai ma’ana. Ya kamata gwamnatoci da sarakunan gargajiya da shugabannin addinai da ƙungiyoyin farar hula da sauran al’umma su goyi bayan sake buɗe tattaunawa tsakanin ECOWAS da ƙawancen ƙasashen Sahel (AES). Tarihin da suke da shi tare, tattalin arzikin su da ya cakuɗu da kuma muradun tsaro na bai-ɗaya suna buƙatar hakan. Afrika ta Yamma za ta fi ƙarfi idan tana tare. Ya dace a sake gina mu’amalolin da suka lalace. Mu zama tsintsiya maɗaurin ki ɗaya.
