Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kwamishiniyar Harkokin Mata ta Jihar Neja, Hajiya Hadiza Kuta, ta tabbatar da kama wani jami’in rundunar ’yan sandan Nijeriya da ke aiki a Hedikwatar Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja bisa zargin yi wa wata yarinya mai shekara 13 fyaɗe.
Rahotanni sun nuna cewa an kuma kama wasu mutum biyu da ake zargi da aikata irin wannan laifi a kan yarinyar.
Hajiya Kuta ta bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da manema labarai a ofishinta da ke Minna ranar Litinin.
A cewarta, ana zargin mutanen uku sun riƙa yi wa yarinyar fyaɗe sau da dama kafin daga bisani aka kai ƙorafin lamarin ga Ma’aikatar Harkokin Mata ta jihar.
Kwamishiniyar ta ce iyayen yarinyar ne suka kai ƙarar lamarin ga ma’aikatar domin neman taimako, abin da ya kai ga cafke waɗanda ake zargin.
Ta bayyana cewa iyayen yarinyar sun shaida wa ma’aikatar cewa duk ƙoƙarin da suka yi na neman adalci yana fuskantar cikas, lamarin da ya sa suka nemi sa hannun gwamnati.
“Sun gaya mana cewa ana hana su samun adalci a kai a kai, shi ya sa suka nemi taimakon ma’aikatar,” inji ta.
Hajiya Kuta ta nuna damuwa kan yadda ake ci gaba da samun ƙaruwar rahotannin fyaɗe da suka shafi ƙananan yara da matasa mata a jihar. Ta kuma yi tir da abin da ta kira yunƙurin karkatar da hankalin jama’a daga ainihin zargin fyaɗen ta hanyar zargin yarinyar da satar dabbobi. A cewarta, waɗanda ake zargin sun samu damar aikata laifin ne bayan sun sayi kaji daga hannun yarinyar.
Kwamishiniyar ta jaddada haɗarin talla da yawo da yara mata ke yi a tituna, tana mai cewa hakan na ƙara jefa su cikin haɗari. Haka kuma ta nuna damuwa kan yadda ake bai wa wasu da ake tuhuma da laifukan fyaɗe beli jim kaɗan bayan gurfanar da su a gaban kotu. Ta ce, irin waɗannan matakai kan tauye damar waɗanda abin ya shafa da iyalansu wajen samun adalci, tare da ƙarfafa gwiwar masu aikata irin waɗannan laifuka.
“Abin takaici ne ganin cewa irin waɗannan laifuka kan haifar da mummunan rauni na tunani ga yara, wanda ke lalata burinsu na ilimi da makomarsu. Makomar waɗannan yara na iya lalacewa gaba ɗaya sakamakon ayyukan masu aikata irin waɗannan laifuka,” inji ta.
Kwamishiniyar ta tabbatar wa iyalan yarinyar cewa ma’aikatar za ta bi duk hanyoyin da suka dace domin tabbatar da an yi musu adalci. Ta bayyana cewa, a matsayin wani ɓangare na matakan kariya, an fitar da yarinyar daga al’ummarta tare da mayar da ita wurin da za a kula da lafiyarta da tsaronta.
Hajiya Kuta ta ƙara da cewa yarinyar za ta samu cikakkiyar kulawar lafiya, binciken lafiyar kwakwalwa, shawarwari daga ƙwararru da sauran tallafin da za su taimaka wajen tantance illolin da ta fuskanta da kuma taimaka mata wajen murmurewa.
Ta kuma jaddada muhimmancin gudanar da cikakken bincike kan lamarin, tana mai cewa irin tuhumar da za a gurfanar da waɗanda ake zargi da ita ce za ta ƙayyade ƙarfin shari’ar a gaban kotu.
A ƙarshe, Kwamishiniyar ta ce ma’aikatar na fatan adalci zai yi nasara a wannan shari’a, tare da sake tabbatar da aniyarta ta kare haƙƙoƙi da walwalar waɗanda suka faɗa cikin irin waɗannan matsaloli.
