Mata huɗu da yara biyu sun tsere daga hannun ‘yan bindiga a Katsina

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Wasu mata huɗu da yara biyu sun tsere daga hannun ‘yan bindiga bayan sun shafe kwanaki a tsare, inda dakarun Rundunar Sojojin Nijeriya suka ceto su a yankin ƙaramar hukumar Faskari da ke Jihar Katsina.

A cikin wata sanarwa da kakakin Birged ta 17, Kyaftin Abayomi Adisa, ya fitar, ya ce dakarun rundunar sun gano mutanen a yankin Unguwar Doka a ranar 29 ga Yuni, yayin da suke yawo cikin daji bayan sun tsere daga hannun masu garkuwa da mutane.

Binciken farko ya nuna cewa ‘yan bindigar sun yi garkuwa da su ne daga Unguwar Lado da ke ƙaramar hukumar ƙanƙara tun ranar 22 ga Yuni.

Sanarwar ta ce dakarun sojojin sun ba waɗanda aka ceto kulawar gaggawa, abinci da sauran kayan buƙata, kafin daga bisani suka haɗa su da iyalansu.

Kwamandan Birged ta 17, Birgediya Janar Ishaya Ibrahim, ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da kai hare-hare kan ‘yan ta’adda da sauran miyagu domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ya kuma jaddada cewa Rundunar Sojojin Nijeriya za ta ƙara ƙaimi wajen tabbatar da zaman lafiya da inganta tsaro a faɗin Jihar Katsina.

By ukarofi

Leave a Reply