
Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Gwamnatin Jihar Kebbi ta raba motoci guda 110 na taki da kuma ton ɗari na irin zamani ga manoma 120,000 don noman damina na wannan shekara.
Wannan yana daga cikin kudurran gwamna Malam Nasir Idris na haɓaka harkokin noma da kuma sauƙaƙa wa al’umma rage tsadar rayuwa musamman abinci a jihar.
Gwamna Malam Nasir Idris ya bayyana cewa sanin kowa ne kashi tamanin na al’ummar jihar Kebbi sun dogara ne da noma saboda haka sun fi buƙatar tallafi a wannan ɓangaren, an kuma yi tsarin rabon takin da irin ta yadda zai isa ga ainihin manoman gaskiya daga mazaɓu 3,743 da akwai faɗin jihar Kebbi ba tare da ƴan baranda sun shiga tsakani ba.
Gwamna Malam Nasir ya bayyana cewa gwamnatinsa ta raba ƙananan motocin noma na hannu 10,000 (Power Tiller), injinan ban ruwa masu aiki da hasken rana dubu goma sha biyar, da kuma injinan ban ruwa masu aiki da fetur 10,000 ga manoma kuma kyauta domin ƙara ba su ƙwarin gwiwa wajen gudanar da ayukan noma ta yadda za a ƙara samun abinci.
Haka kuma, ya bayyana cewa gwamnatinsa tana aiki kafaɗa da kafaɗa da jami’an tsaro wajen ganin an sami zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya.


