Daga MUHAMMAD SADISU ABUBAKAR Birnin Kebbi
Gwamnatin Jihar Kebbi ta ƙaddamar da aikin gona na daminar bana, a yayin da ta rarraba ton 6000 na takin zamani da ton 100 na ingantaccen irin shukawa, ga manoma kyauta.
Da yake gudanar da bikin, a Birnin Kebbi, ranar wannan Larabar, Gwamna Nasir Idris, ya ƙara jaddada wanzar da tsarin gwamnatinsa na samun yalwar abinci, ta hanyar bai wa manoma taimakon da ya wajaba.
Ya ce aikin gona shine ƙashin-bayan tattalin arzikin Jihar Kebbi, domin fiye da kashi 80 na al’ummar Jihar manoma ne.
Gwamnan ya ce gwamnati ba zata bari manoma kadai su rika fuskantar ƙalubale na canjin yanayi ba, dalili ke nan ta sawo ingantaccen iri na gero da shinkafa, domin su suka dace da tsarin gwamnati na magance lamarin, ba tare da wani aibi ba.
Kwamred Idris yana mai bada tabbacin cewar gwamnati ta ƙirƙiro da dabarun sauƙaƙa nauyin da manoma ke fuskanta wurin aikin gona, sannan kuma ta sauƙaƙa masu wani ƙalubale na canjin yanayi, sannan kuma ta ƙarfafa hanyoyin noman zamani na tarakta da makamantarsu.
Gwamnan ya ce ya ƙaddamar da rarraba ton 6000 na takin zamanin NPK, da kuma ton 100 na ingantaccen iri, wanda manoma 120,000 za su amfana da su, yana mai cewar gwamnatinsa a tsaye ta ke ta kyautata rayuwar manoma.
A nasa jawabin, kwamishinan aikin gona na Kebbi, Shehu Mu’azu, ya ce wannan shekarar ta 2026, itace shekara ta huɗu a jere, manoma a Jihar Kebbi suna cin moriyar takin zamani da sauran kayayyakin aikin gona kyauta, a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Nasir Idris, da nufin haɓaka abinda manoma ke nomawa.
Shi kuma sakataren gwamnati, Yakubu Bala Tafida, ya ce an kafa kwamitocin da za su yi rabon takin zamanin, da kuma ingantaccen iri, domin tabbatar da cewar waɗanda aka ayyana za su amfana, ya kai garesu.
