Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamna Raɗɗa ya amince da gina tituna masu tsawon Kilomita 20.37 a wasu sassan Jihar. Ya kuma kafa sashen ƙirƙire-ƙirƙire na matasa.
Ya kuma amince da wasu ayyuka da dama na raya ƙasa da suka haɗa da rage kuɗaɗen sabunta lasisi da tantance makarantu masu zaman kansu da kashi 33% da 40%.
Ya amince da ayyukan magance ambaliyar ruwa a anguwani 37 da kuma samar da ruwan sha a garuruwan Rimi da Safana.
Gwamna Dikko Raɗɗa, ya amince da wasu manufofi da ayyukan raya ƙasa domin bunƙasa ƙirƙire-ƙirƙire na matasa, inganta ilimi, faɗaɗa ababen more rayuwa, ƙarfafa samar da ruwan sha, magance ambaliyar ruwa da kuma kare mata da yara ƙanana a faɗin jihar.
Dikko Raɗɗa ya amince da waɗannan matakai ne a yayin taro na 10 na majalisar zartarwa ta Jihar Katsina da ya gudanar a ɗakin taro na gidan gwamnatin Katsina, ƙarƙashin jagorancin gwamnan.
Da yake yi wa manema labarai bayani bayan kammala taron, kwamishinan yaɗa labarai, Dakta Bala Salisu Zango, ya bayyana cewa majalisar ta amince da muhimman takardu da dama da ke da nufin samar da ci gaba mai ɗorewa da kuma inganta ayyukan gwamnati a jihar.
Ya ce majalisar ta amince da kafa sashen ƙirƙire-ƙirƙire (Innovation Unit) a cibiyar koyon sana’o’in matasa ta Katsina, ƙarƙashin ma’aikatar ilimi mai zurfi, da koyar da sana’o’i da fasaha.
A cewarsa, sabon sashen zai zama cibiyar fasaha, ƙirƙire-ƙirƙire da bunƙasa harkokin kasuwanci, domin bai wa matasa damar haɓaka basirarsu da zama masu ƙirƙira da dogaro da kai.
Kwamishinan ya ƙara da cewa “Wannan sashi zai bai wa matasa ilimin ƙwarewa da damar da za ta taimaka musu wajen ƙirƙire-ƙirƙiren, kasuwanci da ci gaban fasaha, wanda hakan zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin Jihar Katsina.”
Dakta Bala Zango ya kuma bayyana cewa majalisar ta amince da rage kuɗaɗen sabunta lasisi da sake tantance makarantu masu zaman kansu bayan buƙatar da ƙungiyar masu makarantu masu zaman kansu ta ƙasa ta gabatar.
Sabon tsarin ya rage kuɗin sabunta lasisin daga Naira 210,000 zuwa Naira 140,000.
Sake tantance makarantu daga Naira 200,000 zuwa Naira 120,000.
Ya ce wannan mataki zai taimaka wajen ƙaruwar ayyukan yi da riƙe ƙwararrun malamai da kuma inganta ilimi a makarantu masu zaman kansu a faɗin jihar.
Ya ƙara da cewa wannan ya nuna ƙudirin Gwamna Raɗɗa na tallafa wa makarantu masu zaman kansu tare da tabbatar da samun ingantaccen ilimi ga al’umma.
Kwamishinan albarkatun ruwa, Alhaji Mannir Ayuba Sullubawa, ya bayyana cewa majalisar ta amince da bayar da kwangilar ayyukan kariya daga ambaliyar ruwa da zaizayar ƙasa a garuruwa 37 na jihar.
Ya ce an ɗauki wannan mataki ne domin rage illar ambaliyar ruwa a yankunan da hukumar hasashen yanayi ta Najeriya (NiMet) ta bayyana a matsayin masu haɗari a daminar bana ta shekarar 2026.
A cewarsa:
“Wannan mataki ne na rigakafi domin kare rayuka da dukiyoyi tare da rage illolin ambaliyar ruwa a yankunan da abin ya shafa.”
Shi ma Kwamishinan ayyuka, gidaje da sufuri, Injiniya Sani Magaji Ingawa, ya bayyana cewa majalisar ta amince da gina manyan titunan cikin garuruwa da suka haɗa da titin Mashi mai tsawon kilomita 3.0 (za a mayar da shi titin layi biyu).
Titunan cikin garin Bakori masu tsawon kilomita 6.67 da titunan cikin garin Malumfashi masu tsawon kilomita 10.7.
Ya ce waɗannan ayyuka na daga cikin ƙudirin gwamnatin Raɗɗa na faɗaɗa hanyoyi da inganta zirga-zirga a manyan garuruwa.
Ya ce”Ayyukan titunan za su inganta sufuri, bunƙasa harkokin kasuwanci da kuma sauƙaƙa rayuwar al’ummar yankunan da za su ci gajiyarsu.”
Haka kuma kwamishinan albarkatun ruwa ya bayyana cewa majalisar ta amince da ƙarin kwangila domin samar da ruwan sha ga garuruwan Rimi da Safana, a matsayin ƙarin aiki ga shirin samar da ruwa na Zobe kashi na 1B.
Ya ce aikin zai tabbatar da wadataccen ruwan sha mai tsafta ga al’ummomin yankunan.
Ya ƙara da cewa:
“Samar da tsaftataccen ruwan sha na ci gaba da kasancewa cikin manyan manufofin wannan gwamnati.”
A nata ɓangaren, kwamishiniyar harkokin mata, Hajiya Aisha Aminu Malumfashi, ta bayyana cewa majalisar ta karɓi tawagar wayar da kai daga ƙungiyar matan gwamnonin Najeriya kan hanyoyin ƙarfafa yaƙi da cin zarafin mata da ‘ya’ya mata (GBV) a jihar katsina.
Ta ce tawagar ta samu jagorancin uwargidan gwamnan Jihar Katsina, Hajiya Zulaihatu Dikko Raɗɗa, tare da jami’an ƙungiyar gwamnonin Najeriya da kuma gidauniyar Ford Foundation.
A cewarta, Gwamna Raɗɗa ya sanya hannu kan wata sanarwar haɗin gwiwa da ke jaddada ƙudirin gwamnatin jihar na gina al’umma mai aminci da adalci, inda mata da ‘ya’ya mata za su rayu ba tare da fuskantar tashin hankali, cin zarafi ko nuna wariya ba Inji kwamishiniyar.
“Gwamnan ya sake tabbatar da aniyar gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da manufofi da shirye-shiryen kare haƙƙi da mutuncin mata da ‘ya’ya mata tare da ƙarfafa hukumomin da ke yaƙi da cin zarafin jinsi a jihar,”ta ce.
Majalisar ta bayyana cewa waɗannan matakai suna nuna ƙudirin Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa na ci gaba da bunƙasa matasa, ilimi, ababen more rayuwa, samar da ruwan sha da kuma gina Jihar Katsina mai ci gaba da wadata.
