Za mu tanadar wa Fulani burtali a Augie – Yahaya Muhammed

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Shugaban ƙaramar hukumar Augie Honarabul Yahaya Muhammed Augie ya sha alwashin yi wa Fulanin da aikin hanya ya taɓa burtalin su adalci kamar yadda doka ta tanada.
Ya yi wannan bayanin ne ranar Larabar nan bayan da waɗansu fulani suka yi ƙorafi a kan wani aikin hanya da ta haɗa ƙauyen Gidan-koni da babbar hanyar da ta haɗa ƙaramar hukumar mulki ta Augie zuwa jihar Sokoto ya taɓa burtalin su.

Honarabul Yahaya Augie ya nemi Fulanin da su kwantar da hankalin su ba za a bari wani ƙaramin abu ya zo ya ɓata daɗaɗɗiyar dangantakar da suka tarar tun kakanni da iyaye ba.
Sanin kowa ne gwamnati ta tanadi burtalin shanu a ko ina faɗin ƙasar nan saboda haka su ma duk inda aikin ya taɓa za a nemo wata hanyar nema musu wata mafita saboda su ma ƴan ƙasa ne suna da ƴanci kamar kowa.
Ya yi kira ga al’umma da su guji yaɗa labaran ƙarya domin haddasa fitina tsakanin al’umma kuma duk wanda aka samu da laifin ruruta wuta don a yi tashin hankali ba mu lamunce shi ba. “Inji shi”

By ukarofi

Leave a Reply