
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaban Kamfanin Optimal Image Media Limited da gidan talabijin na 3rd Eye Africa, Alhaji Shuaibu Mungadi, ya yaba wa Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris bisa irin nasarorin da gwamnatinsa ta samu wajen inganta tsaro da kuma aiwatar da ayyukan ci-gaba a sassan jihar.
Mungadi ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin da tawagar yaɗa labaran gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu, Alhaji Yakubu Ahmed BK ta kai masa ziyarar wayar da kai a ofishinsa da ke Abuja.
Ya bayyana cewa, ayyukan gwamnan sun cancanci yabo, waɗanda daga cikinsu akwai sauya fasalin Birnin Kebbi tare da ɗaga martabar jihar gaba ɗaya.
A cewarsa, Gwamna Nasir Idris ya nuna ƙwazo wajen magance matsalar tsaro ta hanyar samar wa hukumomin tsaro kayan aiki da tallafin da suka dace, abin da ya taimaka wajen rage ayyukan masu aikata laifuka da inganta zaman lafiya a jihar.
Mungadi ya ce nasarorin da gwamnatin ta samu sun samo asali ne daga jajircewar Gwamnan wajen gudanar da mulki nagari da kuma kusancinsa da al’umma.
Ya kuma yi alƙawarin cewa, Optimal Image Media da 3rd Eye Africa TV za su cigaba da yaɗa ayyukan alherin gwamnatin Kebbi gami da ƙaryata dukkan wani yaɗa labaran ƙarya ko ƙoƙarin bata sunan gwamnatin.
A nasa jawabin, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu, Alhaji Yakubu Ahmed BK, ya gode wa 3rd Eye Africa TV bisa cigaba da nuna ayyukan gwamnatin Gwamna Nasir Idris.
Ya ƙara da cewa, ziyarar na da manufar ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin kafar yaɗa labaran da gwamnatin jihar domin ci gaba da isar da sahihan bayanai ga al’umma.
Kwamishinan ya ƙara da cewa gwamnatin ta samu gagarumar nasara a fannoni da dama, ciki har da gina da gyaran hanyoyi, gyaran makarantu, asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko, tare da aiwatar da sauran ayyukan raya ƙasa a dukkan ƙananan hukumomi 21 na faɗin jihar.
