Daga JAMIL GULMA a Kebbi
A wani muhimmin mataki na ƙarfafa ayyukan addinin musulunci da tallafa wa malamai, tsohon gwamnan Kebbi kuma sakataren tsare-tsare na jam’iyyar APC ta ƙasa Alhaji Sulaiman Muhammad Argungu, Jarman Kabi, ya sadaukar da gida mai ɗakuna huɗu ga ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’iqamatis Sunnah (JIBWIS), reshen ƙaramar hukumar mulki ta Argungu.
Ya ce bisa ga la’akari da yadda manyan malamai ke zuwa garin Argungu wajen al’amurran addini ne ya sanya shi sadaukar da wannan gidan a matsayin masaukin baƙi ga kungiyar domin saukar da malamai da baƙi masu zuwa gudanar da wa’azi da sauran ayyukan addini.
Kafin miƙa gidan mai ɗakuna huɗu ya samar da duk kayan da a ke buƙata da suka haɗa da gadaje, katifu da sauran kayan amfani da kuma samar da masallaci a cikin harabar gidan, da ɗakin mai gadi, tare da wutar solar mai aiki na tsawon sa’o’i 24 domin tabbatar da ingantaccen yanayi ga duk masu amfani da gidan.
An gudanar da miƙa makullan gidan ga shugabannin JIBWIS Argungu ta hannun Alhaji Kabiru Maiarewa (Uban Kasar Sarka) tare da shugaban gidauniyar Jarman Kabi, Alhaji Ibrahim Yahaya, a madadin maigirma Jarman Kabi.
