Rikicin ƙyamar baƙi a Afirka ta Kudu ya tilasta wa ‘yan Nijeriya da wasu tserewa

Spread the love

An fara zanga‑zangar ƙyamar baƙi a sassa daban‑daban na Afirka ta Kudu, lamarin da ya sa aka jibge jami’an tsaro saboda fargabar rikice‑rikice.

Shugaba Cyril Ramaphosa ya buƙaci masu zanga‑zangar su guji tashin hankali, yana mai jaddada cewa dole ne a gudanar da zanga‑zanga cikin lumana ba tare da tsoratarwa ba.

Zanga‑zangar na da alaƙa da wa’adin da wasu ƙungiyoyi suka bai wa baƙin da ba su da takardu su fice daga ƙasar.

Hakan ya sa mutane da dama suka fara tserewa saboda tsoron hare‑hare, yayin da hukumomi suka ce an riga an mayar da sama da mutum 25,000 kasashensu, yawancinsu daga wasu ƙasashen Afirka.

A birnin Johannesburg, inda ake gudanar da wasu daga cikin zanga‑zangar, an samu tsaiko a harkokin yau da kullum, inda shaguna da dama suka rufe, kuma aka samu yanayi na tsoro da shiru.

Dubban baƙi kuma na cigaba da jiran a kwashe su a sansanonin wucin gadi domin tsira da lafiyarsu.

A gefe guda, Shugaba Ramaphosa ya tunasar da jama’a cewa baƙin da ke zaune bisa doka na da haƙƙi kamar kowa, yana mai cewa suna taka muhimmiyar rawa wajen gina tattalin arziƙin ƙasar.

A Durban kuwa, ana rushe sansanonin da ke ɗauke da ‘yan Malawi, yayin da wasu ke bayyana takaicinsu na barin iyalansu da rayuwar da suka fara ginawa sakamakon matsin lamba da matsalar tsaro.

By Babaji