
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Tarayya ta umarci a yi wa tsarin ilimin Nijeriya garambawul, sakamakon rahoton da ke nuna cewa kusan ɗalibai miliyan 20 sun fice daga makaranta.
Ministan Ilimin, Dakta Tunji Alausa ne ya sanar da haka yayin ƙaddamar da Kwamitin Ministoci na Aiwatarwa da Sanya ido na Hukumar Ilimin Bai-ɗaya (UBEC) a Abuja.
Ya ce, tsarin raba raba makarantar sakandare ƙarama, wato Junior Secondary School (JSS) da Senior Secondary School (SSS) ya gaza samar da mafita ga yawan ɗaliban da ba sa zuwa makaranta.
A madadin haka, ya ce za a samar da wani tsari a zaman da za a yi na Kwamitin Zartarwa akan Ilimi da zai wakilci wanda ake shirin rushewa.
Rahotanni sun bayyana cewa matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na inganta samun damar ilimi da kuma rage yawan ɗaliban da ke barin makaranta ba tare da kammalawa ba.
Manufar sauyin ita ce sauƙaƙa tsarin karatu, inganta sakamakon koyo, da kuma rage matsalolin da ke hana yara ci gaba daga matakin farko zuwa na gaba.
Haka kuma, ana sa ran sabon tsarin zai taimaka wajen ƙara yawan yara da ke kammala karatu a matakin sakandare, tare da inganta ingancin ilimi a faɗin Nijeriya.
