Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina
Hamshaƙin ɗan kasuwa Alhaji Dahiru Bara’u Mangal ya yi kira ga masu hali da su shigo su tallafawa harkar Ilimi musamman a manyan makaratun jihar.
Mangal ya yi wannan kira ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin hukumar gudanarwa na jam’iar FUDMA da ke Dutsinma a Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban jam’iar Farfesa Muhammadu Khalid Usman a gidansa da ke garin Katsina.
Ya nuna jin daɗin sa ganin yadda yaga yan jihar Katsina da ke riƙe da manyan muƙamai a gwamnatin tarayya da na jihar da sauran ma’aikatu masu zaman kansu waɗanda suka kammala karatu a jami’o’in FUDMA da jam’iyar Umaru Musa Yar’adua a Dutsinma da Katsina.
Kan buƙatar da mataimakin jam’iar FUDMA ya yi na taimakwa sassan bincike na jam’iar, Dahiru Mangal ya yi alƙawarin duba yiwuwar tallafawa wasu sassan binciken a matsayin gudunmuwar sa na bunƙasa harkar ilimi a jami’o’in da ke jihar.
Haka kuma dangane da taron yaye ɗalibai da mataimakin shugaban jam’iar Farfesa Muhammadu Khalid ya miƙa goron gayyata da gabatar da ƙasida kan kasuwanci kuwa Alhaji Dahiru Mangal ya buƙaci a sanar da shi akan lokaci domin ya yi kyakkyawan shiri.
Tunda farko a jawabin sa, mataimakin shugaban jam’iar Farfesa Muhammadu Khalid Usman ya ce sun kawo ziyara ne domin hada gwiwa tsakinin jam’iar da wasu kamfanoni Mangal da zai inganta sashin kasuwanci na jam’iar.
Farfesa Muhammadu Khalid ya yaba wa wa ɗan kasuwar bisa yadda yake tallafawa alumma musamman mabuƙata a kullum.
