Gwamnatin Katsina ta ja hankalin jama’a da su guji yaɗa labarai da za su taimaka wa ‘yan ta’adda

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa, ya ja hankalin jama’a a kan su guji yaɗa labarun da za su taimaki ko ƙarfafi ‘yan ta’adda da suka addabi jama’a.

Gwamnan ya bada misalin abinda ya faru a lokacin da ‘yan bindiga suka sace Marigayi Manjo Janaral Rabe Abubakar, ya ce dagula al’amura ƙwarai, gami da ƙara ƙarfafa ‘yan ta’addar ƙarfin gwiwa.

Dikko Raɗɗa wanda ya sami wakilcin mataimakin sa, Malam Faruk Lawal Joɓe, a lokacin taron lacca da baje kolin daftarin nasarorin da gwamnatin Dikko Raɗɗa ta samu a cikin shekaru uku.

Taron laccar dai ƙungiyar gamayyar malaman manyan makarantu ta shirya.

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnati za ta cigaba da zage damtse a bisa ƙoƙarin da ta ke na kawo ƙarshen matsalar tsaro da ayyukan ‘yan ta’adda a faɗin jihar.

Ya bayyana nasarorin da gwamnatin sa ta samu a ɓangarori da dama da su ka haɗa da gina makarantu da ɗaukar malaman makaranta sama da 10,000 da kuma ɗaukar ma’aikatan kiwon lafiya domin al’umma.

Gwamnan ya godewa ƙungiyar gamayyar malaman bisa goyon bayan su ga gwamnati mai ci a yanzu, da kuma bin sawun ƙoƙarin da gwamnatin ta yi na gudanar da ayyuka.

Ya bayar da tabbacin cewa, gwamnatin za ta cigaba da ƙoƙarin da ta ke, kuma ba za ta ba su kunya ba a bisa wannan goyon baya na su.

Shugaban taron kuma tsohon mataimakin gwamnan jihar Katsina, Alhaji Tukur Ahmed Jiƙamshi, ya lura da cewa malaman manyan makarantun na cigaba da bayar da goyon baya ga Gwamna Raɗɗa tun daga farkon tafiyar shi a shekara ta 2023.

Alhaji Tukur Jiƙamshi ya yi na’am da cewa gamayyar malaman manyan makarantun na jihar Katsina sun bayar da gudummuwa wajen tsara manufofin gina gobe mai kyau ga jihar Katsina na Dikko Raɗɗa da Faruk Joɓe, wato Building Your Future a turance.

Tsohon mataimakin gwamnan, kuma jagoran kula da manufofin shugaban ƙasa na cigaba wato Renewed Hope Agenda a jihar Katsina, ya bayyana gwamna Raɗɗa a matsayin gogaggen ɗan Siyasa wanda ya ke da ilmi da iya mu’amala da mutane.

Dangane da batun Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kuwa, Alhaji Tukur Jiƙamshi ya tabbatar da cewa ko shakka babu jihar Katsina ta amfana da ayyukan cigaba daga gwamnatin tarayya, musamman a fannonin ilmi da kiwon lafiya da ayyukan gona da tsaro.

Tun da farko shugaban ƙungiyar gamayyar malaman manyan makarantun reshen jihar Malam Nura Abdullahi, ya bayyana cewa a matsayin su na malaman manyan makarantu, sun gudanar da bincike da tattara bayanai a kan abinda gwamnatin ta Dikko Raɗɗa ta gudanar a cikin shekaru uku.

Malam Nura Abdullahi, wanda ya fito daga kwalejin kimiyya da fasaha ta Hassan Usman Katsina, ya yi nuni da cewa bayanan da su ka tattara gami da wallafawa, za su zamo abun dogaro ga sauran ma su bincike a kan gwamnatin ta Raɗɗa.

A jawabin godiya, Malam Samaila Adamu Dangani daga kwalejin kimiyya da fasaha ta Hassan Usman Katsina, ya godewa gwamnati a bisa amfani da shawarwarin da su ka bayar da ma zama da su a wasu lokutan.

A lokacin taron laccar, Dakta Nura Muhammad Ilyasu, daga sashen nazarin addinin musulunchi na jami’ar Umaru Musa Yar’adua, ya gabatar da ƙasida wadda ta ƙunshi cikakkun bayanai na rubutu da hotuna, a kan nasarorin da gwamnatin Dikko da Joɓe ta samu a cikin shekaru uku.

Ƙasidar ta kuma fito da wasu shawarwari daga malaman manyan makarantun da zai taimaki wa gwamnatin wajen ƙara sauke nauyin da ya rataya a wuyan ta.

Haka ma dai ɗaya daga cikin ya-yan ƙungiyar Malam Sa’adu Abdulmumini, daga kwalejin Ilmi ta Isah Kaita, ya yabawa gwamna Raɗɗa a bisa amincewa da ƙarin albashin kashi 25 da 35, wanda a yanzu haka aiwatarwa kawai ya rage.

By ukarofi

Leave a Reply