Daga MUHAMMAD SADISU ABUBAKAR Birnin Kebbi
Gwamnan Nasir Idris ya rarraba Naira miliyan 20 ga waɗanda hatsarin mota ya rutsa da su a Ambursa, da ya yi sanadiyyar rasuwar ‘yan kwallon kafa guda biyar, a yayin da wasu suka samu raunuka.
Ranar Jumu’ar da ta wuce ne, wasu matasa na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Ambursa, suna kan hanyasu zuwa garin Gulumbe, da ke maƙwabtaka da Ambursa, motar Sienna kirar Toyota da suke ciki, ta kife da su, sauran kilomita kaɗan da inda za su tafi.
A nan ta ke, mutane huɗu suka mutu, wani saurayi kuma, guda ɗaya ya-cika a asibiti, sauran kuma akayi masu magani aka sallamesu, suka dawo gidajensu.
A lokacin da hatsarin ya afku, Gwamna Nasir Idris yana cikin jerin-gwanon motocin ayarinsa (na convoy), a kan hanyarsa zuwa filin Jirgin saman Sir Ahmadu Bello da ke Ambursa.
Gwamnan ya tsaya wurin hatsarin, aka yi ceton rayukan waɗanda suka yi hatsarin tare da shi, kuma ya bada umurnin cewar motar ɗaukar marassa lafiya ta kwashe waɗanda hatsarin ya rutsa da su zuwa asibiti a yi masu magani kyauta, aljihun gwamnati.
A ranar wannan Littinin ce, Gwamna Nasir Idris ya aika da ayari mai ƙarfi, ƙarƙashin jagorancin kwamishinan kula da ƙananan hukumomi da masarautu, Garba Umar Dutsinmari, zuwa ta’aziyya ga Uban ƙasar Ambursa, Alhaji Isa Haruna Rasheed, da sauran iyayen waɗanda suka yi hatsarin.
Sauran wakilan ayarin sune, kwamishinan yaɗa labarai da al’adu, Yakubu Ahmed Birnin Kebbi, da kwamishinan ayyuka,
Andullahi Umar Muslim, da kuma mai bai wa gwamna shawara na musamman akan harkokin addini, Imran Usman.
Kwamred Idris ya yi ta’aziyya da tausayawa akan rasuwar waɗannan matasan ‘yan kwallon kafa, yayi addu’ar Allah ya ji ƙan su da rahamar sa.
Gwamnan ya bada taimakon Naira miliyan uku-uku ga dukan iyayen waɗanda suka rasu guda biyar, sannan kuma ya bai wa waɗanda suka samu raunuka mutum uku, naira miliyan guda-guda kowanensu, sannan kuma ya rarraba naira miliyan biyu ga waɗanda suka tsira ba suyi rauni ba a lokacin hatsarin, wanda ya haɗa da mai horas da ‘yan wasa, (Coach), wanda ko kwarzane bai yiba.
A mai da jawabi da yayi, uban ƙasar Ambursa, Alhaji Isa Haruna Rasheed, ya bayyana godiya matuƙa ga Gwamna Nasir Idris dangane da Jin-ƙai da yake yima al’umma da kuma tausayawa, yana jaddada cewar shi da
Jama’ar gundumarsa sun wanzar da ɗa’a da biyayya da goyon baya ga gwamnati mai-ci yanzu.
