Uwargidan gwamnan Zamfara ta yi kira a haɗa kai wajen yaƙi da shaye-shaye

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta yi kira da a gaggauta haɗa kai wajen yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, tana mai cewa wannan mummunar ɗabi’a na ruguza iyali, ɓata makomar matasa, sannan tana barazana ga makomar jihar.

Ta yi wannan kira ne a wajen wani taro na tunawa da ranar duniya ta yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi da safara ta 2026, wanda aka gudanar a babban ɗakin taro na Dr. Garba Nadama, sakatariyar J.B. Yakubu, Gusau a yau Talata.

Hajiya Huriyya ta bayyana wannan rana a matsayin abin tunatarwa cewa shaye shaye ba matsalar lafiya kaɗai ba ce.

“Wannan rana tana tunatar da mu cewa shaye-shayen miyagun ƙwayoyi ba matsalar lafiya kaɗai ba ce, matsala ce ta zamantakewa da ke shafar iyalan mu, al’ummomin mu, kuma mafi muhimmanci, matasan mu,” in ji ta.

A cewarta, ƙaruwar amfani da miyagun ƙwayoyi a tsakanin matasa abu ne na damuwa matuƙa, wanda ke buƙatar ɗaukar mataki cikin gaggawa.

Ta kuma yaba wa masu shirya taron da dukkan masu ruwa da tsaki da suka sadaukar da lokaci, ƙarfi da dukiya a cikin makon da ya gabata wajen yaƙi da matsalar shaye-shaye a cikin al’ummomin jihar Zamfara.

Uwargidan Gwamnan ta jaddada cewa yaƙi da shaye-shaye yana buƙatar mahalartar dukkan sassa na al’umma.

“A matsayin mu na iyaye, malammai, shugabannin addini da na gargajiya, hukumomin gwamnati, jami’an tsaro, ƙungiyoyin farar hula da sauran al’umma, kowa yana da muhimmiyar rawar da zai taka,” In ji ta.

A cewarta, dabarar yaƙin ya kamata ta haɗa da ilmantar da matasa kan illolin shaye-shaye, samar musu da hanyoyin ci gaba masu kyau, da kuma tallafa wa waɗanda suka kamu da matsalar ta hanyar jinyar su da sake haɗa su da al’umma, maimakon nuna musu wariya.

Hajiya Huriyya ta umurci shugabannin matasa da wakilan ɗalibai da su jagoranci yaƙin a matakin ƙasa.

“Ku ɗauki wannan saƙo zuwa makarantun ku, ƙauyukan ku da al’ummomin ku. Ku zama muryoyin da za su ƙarfafa takwarorin ku su guji shaye-shaye, su rungumi neman ilimi, aiki tuƙuru, ɗa’a da rayuwa mai amfani,” in ji ta.

Ta bayyana jin daɗin ta ganin yadda taron ya haɗa masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban, tana mai cewa gabatar da bayanai daga masana da kuma jin labaran waɗanda suka daina shaye-shaye zai ƙarfafa gwiwa da sabunta aniyar mu na wanke jihar Zamfara daga shaye-shaye.

Uwargidan Gwamnan ta ce Gwamnatin Jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal ta himmatu wajen tallafa wa da aiwatar da shirye-shiryen da ke kare matasa da kuma samar musu da damar ci gaba.

“Gwamnati a shirye take wajen ci gaba da tallafa wa shirye-shiryen da ke kare matasa, inganta rayuwar al’umma, da kuma samar da damammakin da za su bai wa matasa damar cimma muradun su,” in ji ta.

Ta yi gargaɗin cewa yaƙin ba zai ƙare da kammala wannan taro ba, inda ta yi kira da a ci gaba da samar da tsarin tallafi mai ɗorewa da ya haɗa da iyali, makarantu, cibiyoyin lafiya, cibiyoyin addini, shugabannin al’umma da kamfanoni masu zaman kansu.

“Tare za mu iya ba wa matasan mu kyakkyawar manufa da damar gina makoma mai kyau,” in ji ta.

By ukarofi