Gwamnatin Katsina za ta raba keke napep na marasa lafiya 361

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya kai ziyarar duba baburan keke napep da ake haɗawa domin rabawa ga dukkan unguwanni 361 da ke ƙananan hukumomi 34 na jihar.

Gwamnan ya gudanar da wannan dubawa ne a harabar Muhammadu Buhari House, inda ake haɗa baburan ƙarƙashin kulawar ofishin mai bai wa gwamna shawara na musamman kan binciken ƙananan hukumomi tare da hukumar kula da bunƙasa lafiyar matakin farko ta Jihar Katsina.

Mataimakin darakta a ofishin mai bai wa gwamna shawara na musamman kan binciken ƙananan hukumomi, Alhaji Mukhtar Shehu, ne ya zagaya da gwamnan wajen duba aikin, tare da yi masa bayani kan yadda ake haɗa baburan da kuma tsarin kula da su bayan an fara amfani da su.

Yayin dubawar, Gwamna Raɗɗa ya tantance ingancinsu, ƙarfi da dacewar baburan domin amfani a yankunan birane da karkara na jihar.

Raɗɗa ya yaba da irin ƙwarewar da aka nuna wajen aikin, tare da umartar masu aikin da su ci gaba da tabbatar da ingancinsu yayin da ake ci gaba da haɗa sauran baburan.

Ana sa ran gwamnatin jihar za ta raba babura 361, (Wards)wato guda ɗaya a kowace mazaɓa daga cikin mazaɓu 361 da ke faɗin jihar.

Wannan shiri na da nufin inganta zirga-zirga, da rage matsalolin sufuri ga al’ummar Jihar katsina mussamman marassa lafiya.

Haka kuma, an tanadi wasu daga cikin baburan domin tallafa wa hukumar kula da bunƙasa lafiya a matakin farko wajen isa ƙauyuka masu nisa, don jigilar magunguna da sauran kayan kiwon lafiya, da kuma sauƙaƙa gudanar da shirye-shiryen wayar da kai da kula da lafiyar al’umma.

Sauran kuma za a bai wa ƙananan hukumomi domin inganta sa ido da hulɗa da al’ummomi.

Gwamna Raɗɗa ya tabbatar da cewa wannan shiri na cikin manufofin gwamnatinsa na bunƙasa yankunan karkara, don tabbatar da samun ingantaccen kiwon lafiya, da samar da ayyukan yi ga matasa.

Gwamnan ya umarci hukumomin da abin ya shafa da su samar da tsari na gaskiya da riƙon amana wajen rabon baburan, don amfani da su da kuma kula da su yadda ya kamata.

By ukarofi

Leave a Reply