
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙasar Norway ta tsallake zuwa zagayen ‘yan 16 a gasar Kofin Duniya da ke cigaba da gudana a Nahiyar Amurka, bayan doke Cote d’Ivoire da ci 2 da 1 a zagayen ‘yan 32.
Wannan shi ne karo ne farko da Norway take samun nasara a irin zagayen bayan sau uku tana yunƙuri, kamar yadda ita ma Ivory ta rasa nasara a wasan farko cikin guda bakwai da ta buga a baya.
A minti na 39 ne ɗan wasa Antonio Nusa ya zura ƙwallo a ragar mai tsaron gida Yahia Fofana, wanda ya ba Norway damar jan ragamar wasan.
Ana tsaka da fafatawa ne sai ɗan wasan gefe na Manchester United Amad Diallo ya farke wa Ivory Coast a minti na 74.
Bayan minti 12 ne Haaland na Manchester City ya zura ƙwallon da ta ba Norway nasarar lashe wasan.
A yanzu, Norway za ta kara da Brazil da ta lashe kofin har sau biyar a tarihinta a filin wasa na MetLife.
