
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Yayin da ake cigaba da fafatawa a gasar Kofin Duniya na 2026, ƙasashen Ingila da Mexico sun haye zuwa zagayen ‘yan 16 bayan nasarorin da suka samu a wasannin ‘yan 32.
Ingila ta samu damar tsallakewa zuwa zagayen ‘yan 16n ne bayan doke Jamhuriyar Kongo da ci 2 da 1 a gasar Kofin Duniya da ke gudana a Nahiyar Amurka.
Da fari, Kongo ce ta samu damar jan ragamar wasan bayan zura ƙwallo guda ta hannun Brian Cipenga a minti na bakwai da fara wasan.
Daga bisani Harry Kane ya farke ana sauran minti 15 a kammala wasan, sannan ya kuma ƙara a minti na 86 duk ta hannun sabon ɗan wasan Barcelona Anthony Gordon, lamarin da ya ba Three Lions damar zuwa zagayen ‘yan 16.
A yanzu dai ƙasar za ta fafata da Mexico a zagayen ‘yan 16 yayin da take cigaba da neman lashe kofin karo na farko tun tsawon 60, kamar yadda ita ma kasar Amurka ta Kudun ke fatan kai wa babban mataki a gasar.
