Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya haramta dukkan nau’in noma a cikin maƙabarta a faɗin jihar nan take.
Gwamnan ya bayar da wannan umarni ne a lokacin da ya kai ziyar aiki zuwa ɗaya daga cikin maƙabartu da ke Gusau a ranar Talata. Ya ce al’adar yin noma a wuraren binne matattu ba za a yarda da ita ba.
Gwamna Lawal ya kuma ba da umarnin cewa a lalata duk wata shuka da aka riga aka yi a maƙabarta ba tare da jinkiri ba.
“Duk wanda aka samu yana noma a cikin maƙabarta, za a lalata shukar sa nan take,” in ji gwamnan yana gargaɗi.
Ya jaddada cewa umarnin ya fara aiki daga lokacin da aka bayyana shi, kuma dole ne a bi shi a dukkanin ƙananan hukumomi 14 na jihar.
A cewar gwamnan, maƙabartu wurare ne masu tsarki na jama’a da aka keɓe domin kiyaye mutuncin matattu da tunawa da su. Yin noma a cikinsu, ya ce, cin zarafi ne ga wurin kuma ya saɓa wa al’adu da darajar addini.
Ya roƙi sarakunan gargajiya, shugabannin al’umma, da hukumomin gwamnati masu alaƙa da su tabbatar an bi umarnin, tare da wayar da kan jama’a kan sabuwar dokar.
Fadar gwamnan ta ce za a tura tawagogin sa ido domin tabbatar da aiwatar da umarnin a faɗin jihar.
