Kwamishinan yaɗa labarai ya ƙaryata wanzuwar kungiyar ‘yan ta’adda a Kebbi

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kebbi Alhaji Ahmed Yakubu Birnin Kebbi ya ƙaryata wanzuwar sabuwar kungiyar ƴan ta’adda da a ke kira “Sai Malam” a jihar.
Kwamishinan ya bayyana cewa rashin samun ainihin sahihin bayani ne ya sanya aka alaƙanta lamarin da ƙungiyar ta’addanci.

Ya bayyana cewa bayan gudanar da ƙwaƙwƙwaran bincike daga jami’an ƴan sanda da kuma DSS an tabbatar da dai kama waɗansu ƴan damfara ta yanar gizo ne da kuma masu ɓata wa mutane suna amma ba su da alaƙa da wata ƙungiyar ta’addanci mai suna “Sai Malam”
Ya yi kira ga ƴan jarida da su rinƙa tantance gaskiyar labari kafin su wallafa saboda yaɗa labaran ƙarya yana iya haddasa tashin-tashina cikin al’umma.

Ya kuma nemi haɗin kan kafafen yaɗa labarai wajen bayyanawa duniya irin ayukan da wannan gwamnati ke yi wa al’ummar jihar Kebbi.

Ya nemi haɗin kan al’ummar jihar Kebbi musamman wajen bai wa wannan gwamnati ta Malam Nasir Idris da hukumomin tsaro wajen kai rahotannin duk wani mutum ko gungun mutane da ba su yarda da su ba.

By ukarofi

Leave a Reply