
An kama tsohon Ministan Ƙirkire-ƙirkire, Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji, a filin jirgin saman Akanu Ibiam International Airport da ke Enugu, yayin da yake shirin hawa jirgi zuwa Abuja a safiyar ranar Laraba.
Rahoton Premium Times ya ce an tsare Nnaji ne domin miƙa shi ga hukumar Yaƙi da Cin-Hanci da rashawa da sauran laifuka masu alaka ICPC domin ci gaba da bincike kan zargin ƙirƙirar jabun takardun karatu.
Ana zargin wannan batu ne ya sa ya yi murabus daga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a watan Oktoban shekarar 2025.
Kamen nasa ya biyo bayan umarnin da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar makonnin da suka gabata, inda ta umarci ICPC da ta kama tsohon ministan bisa zargin yin jabun takardun karatu.
A hukuncin da kotun ta yanke a tsakiyar watan Yuni, ta kuma ba ICPC izinin ayyana Nnaji a matsayin wanda ake nema ta hanyar jaridun ƙasa, kafafen sada zumunta da sauran kafafen yaɗa labarai idan hakan ya zama dole.
ICPC ta shaida wa kotun cewa ta nemi wannan umarni ne bayan Nnaji ya ƙi amsa gayyata da dama da hukumar ta aika masa domin gudanar da bincike kan zarge-zargen.
A watan Oktoban shekarar 2025 ne rahotanni suka fara bayyana cewa ana zargin Uche Nnaji da ƙirƙirar jabun takardar digirinsa ta farko daga Jami’ar Nsukka (UNN), da kuma takardar shaidar kammala bautar ƙasa ta NYSC.
