
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wani masanin harkar shari’a mai suna Hashim Abdullahi ya shiga hannun ‘yan bindiga yayin da yake koma wa gida daga taron ƙasa na Ƙungiyar Lauyoyi Musulmi ta Ƙasa (MULAN) da aka gudanar a Jihar Kano.
Tsohon shugaban MULAN, Sa’idu Muhammad Tudun-Wada ne ya tabbatar da batun a wata sanarwa da jaridar NigerianSketch ta samo a ranar Laraba.
A cewar sanarwar, an yi garkuwa da Abdullahi ne a lokacin da yake kan hanyar koma wa garin da yake zama a Jihar Kebbi bayan halatar taron.
Sa’idu Tudun-Wada ya bayyana cewa, masu garkuwar sun tattauna da iyalai da makusantan lauyan, inda da fari suka nemi a biya su fansar Naira miliyan 200 domin sako shi, sannan da aka nemi su yi rangwame sai suka rage zuwa miliyan N100.
A cewarsa, yanzu ‘yan bindigar suna neman a biya su Naira miliyan 50 da kuma babura guda biyar a matsayin sharuɗɗan sako Abdullahi.
Tsohon shugaban na MULAN ya koka game da faruwar al’amarin inda ya roƙi al’umma musamman lauyoyi da su riƙa sanya tsararren lauyan a addu’o’insu.
Haka kuma, ya yi kira da a gaggauta fitar da shi daga halin domin ya koma cikin iyalansa, yana mai roƙon masu garkuwar da su sako ba tare da wani jinkiri ba.
