Daga AISHA ASAS
Mai karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin Adabi. Sannunku da jimirin bibiyar jaridar al’umma, Blueprint Manhaja.
A makon da ya gabata mun gabatar muku da maƙala mai taken ‘Me ya bambanta marubutan Hausa da na Turanci?’ Inda muka warware muku biri har wutsiya kan bambancin da ke akwai tsakanin rubutun Turanci da na Hausa.
A wannan makon ma ba mu gaji ba, domin za mu tattauna kan yadda rubutu kansa ke iya bayyana wa mai karatu bambancin da ke tsakanin rubutun Hausa da na Turanci. Duk da cewa tarihin adabi da ra’ayoyin masana suna taimakawa wajen fahimtar wannan bambanci, saidai babu abin da ke bayyana shi kamar yadda yake fitowa a cikin ayyukan marubutan kansu.
A cikin adabin Hausa, littafin ‘Ruwan Bagaja’ na Abubakar Imam ya kasance ɗaya daga cikin fitattun ayyukan da suka nuna yadda marubucin Hausa ke amfani da dabarun ba da labari da suka samo asali daga tatsuniya, hikima da kuma al’adar baka. Labarin yana tafiya ne cikin salo mai ɗauke da kasada, darussa da abubuwan mamaki, inda mai karatu ke samun nishaɗi tare da ilmantuwa a lokaci guda.
Masana adabi sun daɗe suna kallon ‘Ruwan Bagaja’ a matsayin wani aiki da ya haɗa tsohuwar hikimar Hausawa da kuma sabuwar hanyar rubutun zamani. A cikin littafin, marubucin ba ya gaggawar kai mai karatu ga ƙarshe. Maimakon haka, yana tafiya da shi a hankali cikin duniyar labari, yana gabatar da darussa, karin magana da hikimomi a hanya.
Irin wannan salo yana da alaƙa da tsohuwar al’adar masu ba da labari a ƙasar Hausa, waɗanda ba kawai suna ba da labari ba ne, har ila yau suna koyarwa da nishaɗantarwa.
A wani ɓangaren kuma, idan aka dubi ayyukan William Shakespeare kamar ‘Hamlet’ ko ‘Macbeth, ana ganin yadda marubucin Turanci ke gina labari a kan rikicin tunani, gwagwarmayar zuciya da kuma sakamakon zaɓin da mutum yake yi.
A cikin waɗannan ayyuka, hankali ya fi karkata ga nazarin ɗabi’ar mutum da abubuwan da ke faruwa a cikin zuciyarsa. Mai karatu ko mai kallo yana bibiyar yadda tunani, kwaɗayi, tsoro ko son mulki ke sauya rayuwar jarumai.
Haka kuma, idan aka waiwayi ayyukan George Orwell kamar ‘Animal Farm’ ko ‘Nineteen Eighty-Four’ (1984), ana ganin yadda marubucin Turanci ke amfani da labari wajen yin sharhi kan siyasa, iko da tsarin mulki. Rubutunsa yana ɗauke da saƙonni masu zurfi, amma ana gabatar da su cikin tsari mai cike da hujjoji da alamu.
Wannan ba yana nufin cewa, marubutan Hausa ba sa yin nazarin ɗabi’ar mutum ko al’amuran siyasa ba ne. Haka kuma ba yana nufin cewa, marubutan Turanci ba sa amfani da hikima da salon tatsuniya ba ne. Sai dai abin da bincike ya nuna shi ne, akwai wasu siffofi da suka fi bayyana a cikin kowane adabi sakamakon tarihin da ya haife shi.
Ra’ayin masana kan makomar adabin Hausa:
A cikin shekaru da dama da suka gabata, masana sun yi hasashen cewa, bunƙasar ilimi da fasahar sadarwa za su canza yanayin adabin Hausa. Wannan hasashe yana ƙara tabbata a yau.
Yawan marubutan Hausa masu samun ilimi a jami’o’i yana ƙaruwa. Haka kuma ana samun masu nazarin adabi da ke wallafa bincike cikin Hausa da Turanci. Wannan ya sa ake ganin sabon ƙarni na marubutan Hausa yana ƙara haɗa hikimar gargajiya da kuma dabarun bincike na zamani.
Wasu masana suna ganin cewa, wannan haɗuwa za ta iya samar da sabon salo wanda zai kasance na Hausa amma kuma yana iya gogayya da manyan ayyukan adabin duniya.
A gefe guda kuma, akwai masu gargadin cewa, rungumar tsarin rubutu na duniya bai kamata ya sa a manta da ginshiƙan adabin Hausa ba. A cewarsu, abin da ya ba adabin Hausa daraja shi ne kusancinsa da rayuwar al’umma, hikimarsa da kuma ikonsa na isar da saƙo cikin sauƙi.
Saboda haka, ƙalubalen da ke gaban marubutan Hausa na wannan zamani shi ne yadda za su rungumi sabbin dabaru ba tare da rasa asalin abin da ya bambanta su ba.
Ko akwai abin da ya kamata marubutan Hausa su koya daga marubutan Turanci?
Bincike ya nuna akwai abubuwa masu yawa da marubutan Hausa za su iya koya daga takwarorinsu na Turanci.
ɗaya daga cikinsu shi ne ƙarfafa al’adar bincike kafin fara rubutu. Marubutan Turanci da dama suna shafe lokaci mai tsawo suna tattara bayanai, karanta hujjoji da nazarin maudu’i kafin su fara rubuta littafi.
Haka kuma, ana iya ƙara amfani da tsare-tsaren gina labari da ke taimakawa wajen riƙe hankalin mai karatu daga farko har ƙarshe.
Shin marubutan Turanci na da abin da za su iya koya daga rubutun Hausa?
Marubutan Turanci na iya koyon abubuwa masu yawa daga adabin Hausa. ɗaya daga cikin manyan abubuwan shi ne yadda ake haɗa hikima da nishaɗi cikin rubutu ba tare da sa mai karatu ya ji nauyi ba.
Har ila yau, amfani da karin magana, tatsuniya da dabarun isar da saƙo cikin sauƙi na daga cikin abubuwan da suka ba adabin Hausa wani salo na musamman wanda ya bambanta shi da sauran adabai da dama na duniya.
Yayin da duniya ke ƙara zama tamkar ƙauye guda, bambance-bambancen da ke tsakanin marubutan Hausa da na Turanci suna ci gaba da sauyawa. Duk da haka, har yanzu akwai manyan ginshiƙai da ke bambanta kowane adabi.
Marubutan Hausa sun taso ne daga al’adar da ke ɗaukar hikima a matsayin taska, yayin da marubutan Turanci suka taso daga tsarin da ya ba bincike, tsari da nazari muhimmanci sosai.
Sai dai a ƙarshe, babu wanda ya fi wani daraja saboda bambancin salo. Darajar marubuci tana cikin ikon da yake da shi na taɓa zuciyar mai karatu, motsa tunaninsa da kuma barin saƙon da zai rayu bayan an rufe littafi ko an kammala karanta rahoto.
Wannan ne ya sa, ko a Hausa ko a Turanci, babban marubuci shi ne wanda kalmominsa suke ci gaba da rayuwa a zukatan mutane bayan shekaru masu yawa da rubuta su.
Sai dai kuma idan aka dubi yanayin kasuwancin wallafe-wallafe, za a ga cewa akwai wasu dalilai da ke sa marubutan da ke rubutu cikin manyan harsunan duniya su fi samun tagomashi fiye da marubutan da ke rubutu cikin ƙananan kasuwannin harsuna. Daga cikin waɗannan dalilai akwai girman kasuwa, tsarin bugawa da kuma irin goyon bayan da ake ba wa rubuce-rubuce.
Wannan ne ke sa idan marubucin Turanci, wanda kuma ke rubutu cikin harshen da ke da faɗaɗɗiyar kasuwa, ya wallafa aiki ɗaya ko biyu masu karɓuwa, yana iya samun kuɗaɗen shiga da suka zarce abin da yawancin marubuta a wasu harsuna ke samu. Hakan ba wai wani fifiko na baiwa ba ne kawai, sai dai sakamakon tsarin kasuwanci, bugawa da tallafawa marubuta da ke kewaye da aikin.
Idan aka ji cewa wani littafi na Turanci ya sayar da ɗaruruwan dubban kwafi ko ma miliyoyi a ƙasashen waje, akan yi mamakin yadda hakan ke faruwa. Amma idan aka yi nazari kan tsarin da ke bayan irin wannan nasara, za a fahimci cewa akwai wasu muhimman abubuwa da ke taimakawa wajen tabbatar da hakan.
Ana iya fahimtar wannan batu ta hanyar kallon wasu misalai daga abin da ke faruwa a kasuwar littattafan Hausa.
Misali, kafin ma littafin Hausa ya isa hannun marubuci bayan an kammala bugawa, a wasu lokuta wasu kwafi kan fita ta hanyoyi daban-daban ba tare da izinin marubucin ba. Ni karan kaina da nake rubuta wannan maƙala na fuskanci irin wannan ƙalubale a wani littafinna mai suna ‘Uwar Makaranta’ na biyu. A lokacin da nake jiran a kammala aikin bugawa, sai wata mai karatu ta tuntube ni tana yaba wa game da yadda aka ƙare labarin. Wannan kuwa ya ba ni mamaki domin a lokacin an sanar da ni cewa har yanzu ba a kammala aikin ba. Binciken da na yi daga baya ya nuna cewa kwafin littafin ya fita daga wurin da ake gudanar da aikin kafin lokacin da ya kamata.
Bayan fitowar littafi kuma, akwai wasu hanyoyi da dama da ke sa aikin marubuci ya kai ga masu karatu ba tare da hakan ya haifar masa da ribar da ta dace ba. Misali, mutum ɗaya kan sayi littafi sannan ya ba mutane da dama haya ko aro har su karanta shi kafin a ajiye shi ko a sake siyar da shi. Haka kuma akwai cinikayyar tsofaffin littattafai da ke tsakanin masu sayar da littattafai da masu karatu, inda littafi guda zai riƙa sauya hannu sau da yawa ba tare da wani ƙarin amfani ya koma ga marubucin da ya rubuta shi ba.
Wani ɓangaren kuma shi ne na masu samar da sautukan littattafai (audio), inda ake amfani da labarin da marubuci ya kashe kuɗi da lokaci wajen samarwa, amma ribar da ake samu daga hakan ba koyaushe take komawa gare shi yadda ya kamata ba. Sai dai zuwan kafafen zamani kamar YouTube ya fara buɗe wasu hanyoyi da ke ba wasu marubuta damar amfana daga ayyukansu.
Haka kuma, gidajen rediyo sun taka muhimmiyar rawa wajen yaɗa adabin Hausa tsawon shekaru. Sai dai a wasu lokuta, tsarin da ake amfani da shi ba ya tabbatar da cewa marubuci yana samun cikakkiyar moriyar aikin da ake amfani da shi. Misali, a shekarar 2020 lokacin da littafina na ‘Ba Shi Ba Ne’ ya fito, an samu wani yanayi da ya nuna yadda wasu ke kallon amfani da aikin marubuci. Bayan samun amincewar marubuciyar littafin, wato ni kenan, an sake gabatar mani da buƙatar na biya kuɗi domin a karanta littafinta a wani gidan rediyo, duk da cewa hakan zai ƙara wa gidan rediyon masu sauraro da mabiya.
Idan aka tattara waɗannan misalai gaba ɗaya, za a fahimci cewa akwai hanyoyi masu yawa da ake amfana da aikin marubucin Hausa ba tare da cikakkiyar fa’ida ta koma gare shi ba. Da ace kowane ɓangare da ke cin gajiyar aikin marubuci yana biyan haƙƙin da ya dace, babu shakka yawan kuɗaɗen da marubuta za su samu daga littattafansu zai ƙaru sosai.
A gefe guda kuma, marubutan Turanci a wasu ƙasashen duniya suna cin gajiyar tsarin wallafe-wallafe da ya daɗe yana bunƙasa. Akwai manyan kamfanonin bugawa da masu zuba jari ke tallafawa, waɗanda ke da damar ɗaukar aikin marubuci tun daga bugawa har zuwa tallatawa da dillanci. Saboda haka, marubuci na iya mayar da hankali kan rubutunsa, yayin da kamfanin bugawa ke kula da sauran fannoni na kasuwanci.
Wannan kuwa wata dama ce da yawancin marubutan Hausa ba su da ita a yanzu, duk da cewa an taɓa samun wasu ƙoƙari a baya ta hannun cibiyoyi kamar NNPC. Wannan na nuna cewa bunƙasar adabin Hausa ba ta ta’allaka ga ƙwarewar marubuta kawai ba, har ila yau tana da alaƙa da gina ingantaccen tsarin bugawa, kariyar haƙƙin marubuta da kuma samar da kasuwar da za ta ba su damar cin moriyar aikinsu yadda ya kamata.
