Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamna Jihar Katsina Malam Dikko Raɗɗa Ya rantsar da sabbin alƙalan lardi na kotun shari’ar Musulunci ta Jihar Katsina.
Sabbin alƙalan lardin da aka rantsar sun haɗa da Alƙali Ibrahim Abdullahi Yakubu daga ƙaramar hukumar Dandume da kuma Alƙali Bala Salisu Daura daga ƙaramar hukumar Daura.
A jawabin sa bayan kammala rantsar da su, Gwamna Raɗɗa ya taya sabbin alƙalan murna bisa wannan muƙami da aka ba su, yana mai bayyana cewa an ɗora musu babban nauyi na tabbatar da adalci da kiyaye martabar tsarin shari’ar musulunci.
Gwamnan ya buƙaci alƙalan da su gudanar da ayyukansu cikin tsoron Allah, gaskiya, riƙon amana da adalci, tare da kauce wa duk wani abin da zai iya kawo cikas ga mutuncin harkar shari’a.
Ya kuma jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da tallafa wa ɓangaren shari’a domin tabbatar da samar da adalci da kuma ƙarfafa tsarin mulki da shugabanci nagari a Jihar Katsina.
