Kotu ta tabbatar da shugabancin David Mark a ADC

Spread the love

Babbar Kotun Tarayya a Abuja, ta tabbatar da halaccin shugabancin tsagin su Sanata David Mark a jam’iyyar ADC da kuma yin watsi da ƙarar ɗan Majalisar Wakilai, Leke Abejide ta ƙalubalantar naɗin Mark da Rauf Aregbesola a matsayin shugaba da sakataren jam’iyyar na ƙasa.

Mai shari’a Musa Liman ya ce kotun ba ta da hurumin shiga harkokin cikin gida na jam’iyya, sannan ya bayyana cewa Abejide bai nuna cewa an tauye masa wata doka ko haƙƙi ba, kuma bai fara amfani da hanyoyin sasanta rikici na cikin jam’iyyar ba kafin ya garzaya kotu.

Kotun ta kuma yanke cewa miƙa shugabancin jam’iyyar daga Ralph Nwosu zuwa David Mark bai saɓa wa kundin tsarin mulkin ADC ba, tare da tabbatar da cewa zaɓen Mark da Aregbesola ya gudana bisa tanadin kundin tsarin mulkin jam’iyyar, Dokar Zaɓe ta 2026 da kuma sa ido na hukumar INEC.

Haka kuma, kotun ta umarci Abejide ya biya tarar Naira miliyan biyu ga kowane ɗaya daga cikin waɗanda ake ƙara, sannan ta ci tarar lauyansa Naira miliyan 10 bisa tanadin Dokar Zaɓe ta 2026.

By Babaji

Leave a Reply