Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Rundunar ‘yan sanda a Katsina sun ƙwato dabbobi guda 117 daga hannun ‘yan bindiga bayan sun daƙile yunƙurin satar dabbobi a ƙaramar hukumar Charanchi na Jihar Katsina.
A cewar jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu,ya ce bayan da babban jami’in ‘yan sanda na ofishin Charanchi ya sami bayanan sirri na yunƙurin satar dobbobi a ƙauyukan Saburu da Billiri ya jagorancin haɗin gwiwa na sojoji, ‘yan sanda da CWC suka datse hanyar wucewar ‘yan bindigan.
DSP Sadiq Aliyu ya ce bayan musayar wuta ‘yan bindigan suka ranta a na kare ba tare da samun biyan buƙata na satar ba.
Jami’an tsaron sun ƙwato shanu 43 da sauran dabbobi 74 da ‘yan bindigan suka gudu suka bari.
Kwamishinan ‘yan sanda CP Ali Umar Fage ya yaba wa jami’an tsaron bisa nuna ƙwarewa wajan fatattakar ‘yan bindigan,ya jaddada ƙudirin sa na kare rayuka da dukiyar alummar Jihar.
CP Fage ya buƙaci al’ummar jihar da su cigaba da basu goyon baya ta hanyar sanar da su maboyan ɓatagari a faɗin jihar.
