
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wani ƙwararren likita a Jihar Kano ya yanki jiki ya faɗi kuma ya rasu mintina 15 bayan zuwa wajen duba marasa lafiya da suka jima suna jiran sa a wani asibiti.
Mai taimaka wa Gwamnan Jigawa, Sulaiman Harbo ne ya bayyana haka ga jaridar NewsPointNigeria bayan ganin yadda al’amarin ya auku a lokacin da ya kai dattijuwar mahaifiyarsa asibiti domin duba lafiyarta.
Al’amarin ya faru ne a ranar Asabar a Asibitin Arewa Surgery Hospital da ke yankin Hotoro a Ƙaramar Hukumar Nasarawa, inda aka nemi marigayin likitan da ya maye gurbin wani abokin aikinsa da ba ya nan.
Harbo ya ce, ya kai mahaifiyar tasa ce wadda shekarunta su ja, zuwa asibitin da misalin ƙarfe 5 na yammacin ranar bisa alƙawarin da wani likita ya musu.
Ya bayyana cewa, kusan marasa lafiya guda shida da galibinsu sun haura shekaru 80 ne ke jiran likitan a lokacin da al’amarin ya faru.
A cewarsa, bayan isar Dakta Ibrahim asibitin ne jim-kaɗan ya fara jin rashin ƙarfin jiki, lamarin da ya jami’an lafiya irinsa suka garzaya da shi sashen gaggawa, inda acikin mintina 15 aka tabbatar da rasuwarsa.
“Abin takaicin shi ne: dukkan marasa lafiyar da ke jiran ganin likitan sun haura shekaru 80, yayin da ƙwararrun likitoci su kusan biyar suka yi fafutukar ceto ran shi, suka fashe da kuka,” inji shi.
Waɗanda suka shaida mutuwar tasa sun ce kalmomin Dakta Ibrahim na ƙarshe da aka ji su ne, “Laa ilaaha illallah”.
Saidai ba a samu gano ainihin musabbabin yankewar jiki da mutuwar likitan ba a nan take.
