Tinubu ya fi kowane shugaban Nijeriya raya Arewa — Uba Sani

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana cewa Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya fi duk wani shugaban ƙasar da ya gabata aiwatar da muhimman ayyukan ci gaba a yankin Arewa, yana mai cewa manyan zuba jari a fannonin ababen more rayuwa, noma da lafiya sun tabbatar da ƙudirin gwamnatin wajen bunƙasa yankin.

Gwamnan ya kuma yi watsi da ra’ayin da ke cewa Arewa ba za ta goyi bayan sake zaɓen Shugaba Tinubu a zaɓen shekarar 2027 ba, yana mai jaddada cewa shugaban ƙasar zai samu ƙuri’u fiye da waɗanda ya samu a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023.

Uba Sani ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da tashar talabijin ta ARISE TV ranar Talata, inda ya ce kalaman nasa sun ta’allaƙa ne kan bayanai da ƙididdiga masu inganci, ba wai ra’ayin siyasa ko son zuciya ba.

Ya ce, “Ina magana ne bisa hujjoji da ƙididdiga. Zan iya faɗa muku ƙarara cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wa Arewacin Nijeriya fiye da duk wani shugaba da ya taɓa mulkin ƙasar nan.

“Babu wani shugaban ƙasa da ya gudanar da ayyukan ci gaba a Arewa irin waɗanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aiwatar cikin shekaru uku da suka gabata. Wannan magana ce da ta dogara da bayanai da ƙididdiga.”

Dangane da masu cewa farin jinin Shugaba Tinubu ya ragu a Arewa gabanin zaɓen 2027, gwamnan ya ce wannan hasashe ne marar tushe.

“Akwai masu zuwa suna cewa Arewa ba za ta zaɓi Asiwaju ba. Wannan tunani ne kawai na su. Ni Gwamnan Jihar Kaduna ne, kuma ina tabbatar muku cewa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zai samu ƙuri’u fiye da waɗanda ya samu a zaɓen 2023,” inji shi.

Gwamnan ya danganta wannan tabbaci da manyan ayyukan raya ƙasa da gwamnatin tarayya ke aiwatarwa a Kaduna da sauran jihohin Arewa.

Da yake magana kan aikin titin Abuja zuwa Kaduna, Uba Sani ya ce aikin da ya shafe shekaru yana tangal-tangal yanzu ya kusa kammaluwa a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu.

Ya ce, an riga an biya kamfanin da ke aikin sama da naira biliyan 600 daga cikin jimillar kuɗin aikin da ya kai kusan naira biliyan 750, tare da bayyana cewa ana sa ran za a ƙaddamar da titin nan da watan Nuwamban bana.

Har ila yau, gwamnan ya yi tsokaci kan aikin titin Kaduna zuwa Birnin Gwari, yana mai cewa an yi watsi da aikin fiye da shekara 25 kafin gwamnatin Tinubu ta amince da fitar da kuɗin kammala shi.

A cewarsa, makwanni uku da suka gabata shugaban ƙasa ya amince da biyan wani ɓangare na naira biliyan 178 domin gina titin, yana tambayar yadda za a ce al’ummar yankin ba za su yaba da irin wannan ci gaba ba.

A fannin noma kuwa, Uba Sani ya yaba da tallafin da gwamnatin tarayya ke bai wa jihohi, musamman Jihar Kaduna, yana mai bayyana noma a matsayin ginshiƙin tattalin arziƙin jihar.

Ya ce, Kaduna ce ke kan gaba a aiwatar da Shirin Yankunan Sarrafa Kayan Noma na Musamman (SAPZ), sakamakon tallafin da gwamnatin Tinubu ke bayarwa, ciki har da samar da takin zamani domin rabawa manoma ƙanana.

Gwamnan ya kuma lissafo wasu ayyukan gwamnatin tarayya da suka haɗa da kafa Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Tarayya a Kudancin Kaduna, mayar da ɗaya daga cikin asibitocin jihar zuwa Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (Federal Medical Centre), da kuma amincewa da aikin jirgin ƙasa na cikin birnin Kaduna.

Ya ce, a watan da ya gabata ne Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince da ware naira tiriliyan ɗaya domin aikin layin dogo na Kaduna, bayan kammala nazarin yiwuwar aikin da kuma fitar da kuɗaɗen fara aiwatar da shi. Ya ƙara da cewa an kuma ware irin wannan adadi ga aikin layin dogo na Kano.

A ƙarshe, Gwamna Uba Sani ya ce duk waɗannan ayyuka sun nuna ƙudirin gwamnatin tarayya na inganta ababen more rayuwa, faɗaɗa damar tattalin arziƙi da kuma inganta rayuwar al’ummar Arewacin Nijeriya.

By ukarofi

Leave a Reply