Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Tsohon Kansilan unguwar Sabon Gari da ke ƙaramar hukumar Fagge a Jihar Kano, Hon. Chief Fredrick Ilele, ya bayyana cewa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ba ya nuna ƙabilanci ko wariya wajen tafiyar da mulkinsa.
Ilele ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai, inda ya ce salon shugabancin gwamnan ya sa jama’a daga kabilu daban-daban ke ci gaba da ba shi goyon baya.
Ya ce irin wannan tsarin shugabanci ya kuma taimaka wajen ƙara karɓuwa da bunƙasar jam’iyyar a ƙaramar hukumar Fagge da sauran sassan jihar.
Tsohon kansilan ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf zai sake lashe zaɓen gwamna na shekarar 2027, tare da cewa Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ma zai samu gagarumin rinjaye a jihar.
Ya yabawa gwamnan kan ayyukan raya ƙasa da yake aiwatarwa, musamman gine-ginen tituna, magudanan ruwa da kuma sanya fitilun kan tituna a unguwar Sabon Gari.
Haka kuma, ya ce gwamnan na ƙoƙarin inganta tsaro a dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar, tare da kira ga al’ummar Kano da su ci gaba da ba shi haɗin kai da goyon baya domin ci gaban jihar.
A ƙarshe, ya yi addu’ar Allah Ya ci gaba da ba Jihar Kano zaman lafiya da kwanciyar hankali, yana mai cewa abin da gwamnan ya fi buƙata daga al’umma shi ne addu’a.
